'Yan Banga Sun Yi Jina Jina ga 'Yan Bindiga da Suka yi Karon Batta da Dare
- ‘Yan banga a yankin Na’alma, karamar hukumar Malumfashi, sun yi artabu da ‘yan bindiga, inda suka kubutar da mutane
- Bayan karon-batta mai tsanani, ‘yan bindigar sun tsere, sun bar wadansu takalma, kayayyaki da kuma babura a dajin
- Mazauna yankin sun yabawa jarumtar ‘yan bijilanten, tare da bukatar karin tallafi domin karfafa tsaro a yankunan karkara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - ‘Yan bindiga a yankin Na’alma da ke karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina, sun ceto mutum biyu da ‘yan bindiga suka sace bayan fafatawa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bangan sun yi wa ‘yan bindigar kwanton-bauna, inda suka yi artabu mai tsanani har suka tilasta musu gudu.

Asali: Getty Images
Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa bayan arangamar, ‘yan bindigar sun tsere ba tare da nasarar tafiya da mutanen da suka sace ba.

Kara karanta wannan
Sabon salo: 'Yan fashi sun shiga har cikin jami'a, sun yi dalibai fashin kayan alatu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan banga sun farmaki 'yan bindiga
A daren Juma’a ne ‘yan bindiga suka kai hari a yankin Na’alma, inda suka yi awon gaba da mutum biyu daga cikin mazauna yankin.
Sai dai kafin su tsere da su, gungun ‘yan banga na yankin sun far musu, inda suka gwabza fada mai tsanani har suka fatattake su.
A sanadiyyar artabu da ‘yan bangan, ‘yan bindigar sun gudu bayan samun munanan raunuka, inda suka bar wadanda suka sace da kuma babura guda biyu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun bar takalmansu da wasu kayayyaki a wurin yayin da suke kokarin tserewa.
Mazauna yankin sun yabi 'yan banga
Bayan kubutar da mutanen da aka sace, mazauna yankin sun yaba da kokarin da ‘yan bangan suka yi domin kare al’umma daga hare-haren ‘yan bindiga.
Sun ce ba tare da wannan jarumtaka ba, da ‘yan bindigar sun tafi da mutanen da suka sace ba tare da wata tangarda ba.

Kara karanta wannan
"Muna lalata da sama da maza 12 a rana": An ji ta bakin 'yan mata da ke karuwanci
Wasu daga cikin mutanen yankin sun bukaci gwamnati da ta kara tallafa wa kungiyoyin sa-kai domin tabbatar da tsaro a yankunan karkara.
Sun bayyana cewa idan har aka kara ba ‘yan bangan kayan aiki da goyon baya, za su iya dakile hare-haren da ake kaiwa a yankin.
Bukatar karin tallafi domin inganta tsaro
Mazauna yankin Na’alma sun roki hukumomi da su tura karin jami’an tsaro domin taimaka wa wajen yaki da ‘yan bindiga.
Sun bayyana cewa ‘yan bangan na fuskantar kalubale saboda rashin wadatattun makamai da kayan aiki masu inganci.
A cewar wani mazaunin yankin, hadin gwiwar ‘yan sanda da ‘yan bangan zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
An bukaci inganta tsaro a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bukaci jami'an tsaro da su rika sintiri da jiragen sama a iyakokin jihar.
Sanata Bala Mohammed ya ce hakan zai taimaka matuka wajen magance barazanar tsaro da jihar za ta iya fuskanta daga 'yan bindiga da sauran miyagu a Bauchi da kewaye.
Asali: Legit.ng