DSS Ta Mamaye Zauren Majalisa, An Rufe Ofishin Kakakin Majalisa da Mataimaki

DSS Ta Mamaye Zauren Majalisa, An Rufe Ofishin Kakakin Majalisa da Mataimaki

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami’an DSS da ‘yan sanda sun mamaye majalisar dokokin jihar Legas, a safiyar Litinin, 17 ga watan Fabrairu
  • An ce jami'an tsaron sun kuma garkame ofisoshin shugabar majalisar Mojisola Meranda, mataimakinta da sakataren majalisa
  • Wannan na zuwa ne yayin da tsohon shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya shigar da kara a kotu yana kalubalantar sauke shi da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jami’an DSS da ‘yan sanda sun mamaye majalisar dokokin jihar Legas a safiyar Litinin, tare da rufe ofisoshin shugabannin majalisar.

Rahotanni sun nuna cewa an rufe ofisoshin kakakin m ajalisar, Mojisola Meranda, mataimakinta da sakataren majalisar a Alausa, Ikeja.

Jami'an DSS da 'yan sanda sun mamaye zauren majalisar jihar Legas
DSS da 'yan sanda sun dura zauren majalisar Legas, an rufe ofishin kakaki. Hoto: @lshaofficial
Asali: Original

DSS, 'yan sanda sun mamaye majalisar Legas

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa, jami’an tsaron sun mamaye zauren majalisar da misalin karfe 10:00 na safe.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a majalisa, Akpabio ya fusata bayan umartar a yi waje da sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, an ce DSS da 'yan sanda sun mamaye yankin da ginin majalisar yake tare da bincikar mutanen da ke wucewa ta harabar majalisar.

Sai dai an ce shugabar majalisar, Rt. Hon. Meranda ta isa majalisar tare da tawagarta da misalin karfe 11:15 na safe.

Majalisar Legas ta tayar da jijiyoyin wuya

Wata sanarwa daga shafin majalisar Legas, ya nuna cewa, mambobin majalisar sun bayyana matakin da DSS ta dauka a matsayin cin zarafin dimokuradiyya.

Yayin da yake gabatar da batun, Hon. Kehinde Joseph (Alimosho II) ya ce abin da ya faru a majalisar babbar barazana ce ga dimokuradiyya.

"A yau, an shirya fara zaman majalisa da karfe 12 na rana. Amma abin da muka tarar ya ba mu mamaki. Mun ga jami’an DSS a zauren majalisa, wasu suna dauke da makamai masu yawa. Ba mu san dalilin hakan ba," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa 27 sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar APC? an samu bayanai

Dimokuradiyya ba mulkin makamai ba ne

'Yan majalisar Legas sun yi Allah wadai da jami'an DSS suka mamaye zauren majalisar
'Yan majalisar Legas a lokacin da suke kokarin fatattakar jami'an DSS daga zauren majalisar. Hoto: Lagos House of Assembly
Asali: UGC

Wani dan majalisa, Tobun Abiodun, ya ce jaddada cewa mamayar da DSS ta yiwa majalisar barazana ce ga dimokuradiyya.

"Wannan dimokuradiyya ce, ba mulki ne da karfin bindiga ba. An zabe mu don mu wakilci al’umma, kuma muna da wannan hakki..
"Mun yi gwagwarmaya don tabbatar da dimokuradiyya. Abin da ya faru yau cin zarafi ne, kuma mun yi imanin cewa jami’an tsaron da suka aikata hakan ba umarni suka samu ba, sai dai suna kokarin faranta ran wasu masu karfi."
"Idan wani yana jin an tauye masa hakki, to ya garzaya kotu maimakon jami’an DSS su mamaye majalisa. Wannan babban abin kunya ne ga dimokuradiyya."

- Hon. Tobun.

Obasa ya maka majalisar Legas a kotu

Tun farko, tsohon shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, ya maka ‘yan majalisar a kotu, inda yake kalubalantar sauke shi daga mukamin.

Obasa ya shigar da karar ne a babbar kotun jihar da ke Ikeja, yana neman a hanzarta sauraron shari’ar domin mayar da shi kan mukaminsa.

Kara karanta wannan

Bayan tsige babban alkalin jiha, majalisa ta dakatar da mambobi 13 da suka janye

A ranar 13 ga Janairu, 2025, ‘yan majalisa 32 daga cikin 40 suka tsige Obasa a lokacin da yake kasar Amurka.

Majalisa ta fadi dalilin tsige Obasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin Legas ta tsige Mudashiru Obasa bisa zargin almubazzaranci da jefa ‘yan majalisa cikin rikici da juna.

Mojisola Meranda, ‘yar majalisa mai wakiltar Apapa I, ta zama mace ta farko da ta dare kujerar shugabar majalisar Legas bayan tsige Obasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.