Matasa Sun Yi Kukan Kura, Sun Afkawa Wasu 'Yan Fashi a Abuja, An Kashe Mutum 2

Matasa Sun Yi Kukan Kura, Sun Afkawa Wasu 'Yan Fashi a Abuja, An Kashe Mutum 2

  • Fusatattun matasa sun kashe wasu 'yan fashi ne a Abuja bayan da suka yi yiwa wata mata sata tare da hankado ta kasa daga motarsu
  • Wasu shaidun gani da ido, sun ce 'yan fashin sun so halaka matar amma Allah bai nufa ba, sai dai mutane sun yi masu tara tara suka kama su
  • An ce fusatattun matasa sun fara cinnawa daya wuta yayin da suka bi dayan har cikin harabar coci suka jawo shi waje, suka kashe shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fusatattun matasa sun hallaka wasu da ake zargi 'yan fashi ne a kan titin Umaru Musa Yar’Adua, Abuja, bayan sun jefo wata mata daga motarsu.

Lamarin ya faru da misalin karfe 3:00 na ranar Asabar, 15 ga Fabrairu, lokacin da barayin suka jefo wata mata da suka yi wa fashi daga cikin motarsu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ragargaza mai zafi, sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kwato tarin makamai

Fusatattun matasa sun kashe wasu 'yan fashi a Abuja
Matasa sun yi wa 'yan fashi tara tara, sun kashe mutum biyu a Abuja. Hoto: Legit.
Asali: Original

'Yan fashi sun gamu da fushin matasa a Abuja

Bayan kwace mata kayanta, sun tunkudo ta kasa daga cikin motar ba tare da sun tsaya ba. Rahoton ICIR ya nuna cewa ta mota ta kusa murkushe matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Cikin ikon Allah, direban ya samu ya tsayar da motar, bai taka matar ba. Daga nan sai ya bi ‘yan fashin a guje, yana yiwa sauran masu ababen hawa alama."

- A cewar wani ganau.

Ganau din ya shaida cewa direban ya jawo hankalin mutane da masu ababen hawa, inda aka rufarwa 'yan fashi, har aka sha gabansu a wajajen ACO Estate.

Abuja: An cafke tare da kashe 'yan fashi

An ce wasu direbobi sun tare hanyar da 'yan fashin za su juya don komawa Gosa, inda nan take suka fice daga motarsu don tserewa.

'Yan sanda sun cafke wasu gungun mutane da ake zargin 'yan fashin 'one chance' ne
'Yan sanda sun yi holen wasu tarin mutane da ake zargin 'yan fashin 'one chance' ne. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Mutanen da ke wajen, suka bi bayan 'yan fashin tare da cafke su, inda aka fara dukan daya har sai da ya daina motsi, sannan daga bisani aka banka masa wuta.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

Dayan kuma an jefa shi cikin wata kwata. Sai da wani shaidar gani da ido ya lura yana raye, wanda ya jawo hankalin jama'a, aka fara yi masa tambayoyi.

Yadda aka kashe dan uwan dan fashin

Lokacin da aka tambaye shi inda ya fito, ya ce daga jihar Ogun ne kuma shi Bayerabe ne. Amma fusatattun matasan suka soma dukansa.

Ganau din ya shaida cewa matasan sun zuba masa fetur domin kona shi, amma ya yi kokarin tserewa zuwa wani coci, inda suka bi shi har can.

A karshe, matasan sun janye shi daga harabar cocin zuwa wani fili, inda suka rika jifarsa da duwatsu har dai gaji ya mutu.

Wike zai kori direbobin adaidaita a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nyesom Wike ya ba direbobin adaidaita umarnin ficewa daga Abuja, domin dakile barazanar 'yan fashin 'once chance.'

Ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta fara fitar da motocin bas da tasi na haya daga wata mai kamawa a kokarinta na kawo karshen matsalar "one chance".

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun karuwar 'yan fashin kan hanya da ke amfani da motocin haya suka yiwa fasinjoji fashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.