Tashin Hankali: Wasu Fusatattu Sun Cinnawa Jami'in NDLEA Wuta, Ya Kone Kurmus

Tashin Hankali: Wasu Fusatattu Sun Cinnawa Jami'in NDLEA Wuta, Ya Kone Kurmus

  • Jami'in NDLEA, Aliyu Imran, ya kone kurmus a Gadan-Gayan, Kaduna, bayan wani hatsari da ya haddasa mutuwar mutane uku
  • Bayan hatsarin, Imran ya yi kokarin kwantar da tarzoma, amma fusatattun suka soka masa wuka tare da banka masa wuta har lahira
  • Iyalansa sun zargi NDLEA da rashin daukar mataki, amma hukumar ta musanta, tana mai cewa ta tura tawaga don jajantawa iyalan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - A ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, wani jami’in hukumar NDLEA mai suna Aliyu Imran ya rasa ransa a garin Gadan-Gayan da ke karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Rahotanni sun tabbatar da cewa fusatattun matasa sun banka wa jami’in wuta har sai da ya kone kurmus, bayan wani hatsari da ya haddasa mutuwar mutane uku.

NDLEA ta yi magana da fusatattun mutane suka kashe jami'inta a Kaduna
Fusatattu sun cinnawa jami'in NDLEA wuta a Kaduna, ya kone kurmus. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Hatsarin ya faru ne yayin da jami’an NDLEA ke kokarin kama wasu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, inda suka rufa wa motar su baya, inji rahoton SaharaReporters

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya nuna cewa motar da jami’an NDLEA ke bi ta murkushe mutane yayin da direbanta ke kokarin tserewa daga hannun jami’an.

Kaduna: Fusatattu sun babbake jami'in NDLEA

Bayan faruwar lamarin, Imran ya yi kokarin kwantar da hankulan jama’a, amma fusatattun mutane suka kai masa farmaki.

Mazauna yankin sun ruwaito cewa matasan sun soka wa jami’in wuka kafin wani dan sanda ya garzaya da shi asibiti domin ceton rayuwarsa.

Amma fusatattun matasa ba su dakata ba; sun bi su har asibiti, suka janye shi daga ciki, suka cinna masa wuta har sai da ya mutu.

Iyalansa sun nuna rashin jin dadinsu, suna mai cewa hukumar NDLEA ba ta dauki matakin da ya dace ba bayan mutuwar jami’in.

Kaduna: NDLEA ta yi magana kan lamarin

Shugaban NDLEA, Buba Marwa
Hukumar NDLEA ta yi martani ga iyalan jami'inta da aka kashe. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

Sun koka cewa hukumar NDLEA ba ta je musu ta’aziyya ba, kuma ba a yi wani batu kan biyansu diyya ba ko wani hakkin dan uwansu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Sai dai kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya musanta wannan zargi, yana mai cewa hukumar ta tuntubi iyalan marigayin, inji rahoton Daily Trust.

Hakazalika, Babafemi ya bayyana cewa NDLEA ta dakatar da kwamandan da ya jagoranci aikin domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Hukumar ta ce ba za ta lamunci irin wannan tashin hankali ba, tana mai yin kira ga hukumomin tsaro su tabbatar da an yi adalci.

Harin da aka kai wa jami’in NDLEA ya janyo cece-kuce, inda wasu ke kiran a gaggauta daukar mataki don hana aukuwar irin haka a nan gaba.

NDLEA ta gano gonar wiwi a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA a Kano ta cafke wani mutum mai suna Malam Sabo bisa laifin noman tabar wiwi a gonarsa.

Bayan kame shi, Malam Sabo ya kare kansa, yana mai cewa yana noman tabar ne domin amfanin kansa kawai, ba don kasuwanci ba.

NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa an samu ganyen tabar wiwi da aka shuka a gonar Malam Sabo, kuma yana fuskantar tuhume-tuhume bisa karya dokar hana safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.