Dan Najeriya ya soka ma dan Najeriya wuka a kasar India a kan kwanon abinci

Dan Najeriya ya soka ma dan Najeriya wuka a kasar India a kan kwanon abinci

Wani dan Najeriya mai suna Morado mai shekaru 39 a duniya ya gamu da ajalinsa a hannun wani dan Najeriya Samuel bayan ya caka masa wuka a ciki a garin Hennur dake gabashin Bengaluru na kasar India.

Jaridar Times of India ta ruwaito fadan ya kaure tsakanin yan Najeriyan biyu ne a kan wani kwanon abinci da Samuel ya ara daga wajen Morado domin ya sayo abinci a wanai shagon sayar da abinci.

KU KARANTA: Dansanda ya harbi wani mutumi saboda ya auri budurwar da abokinsa yake so

Sai dai a binka da dan adam, koda Samuel ya kammala cin abinci a shagon abincin, sai ya manta da kwanon Morado a shagon, don haka da Morado ya gano hakan, sai ya wanka ma Samuel mari, shi kuma Samuel na tashi ya aikata masa aika aika.

Sai dai rundunar Yansandan yankin ta bayyana cewa: “Samuel da Morado sun tafi bikin party ne a gidan wani abokinsu dake Hennur a daren Juma’a, washegari asabari shi ne Samuel ya ari kwanon Morado domin ya sayo kaza a wani shagon sayar da abincin Afirka.

“Amma sai Samuel ya manta da kwanon abincin a shagon, inda aka kunshe masa kazar a cikin takardar kunshe abinci. Ganin kwanonsa ya bata, sai Morado wanda yake cikin halin maye ya shiga dukan Samuel, da kyar aka shiga tsakaninsu.

“Can bayan komai ya lafa sai Samuel ya wanki kafa ya tafi gidan Morado dake unguwar Janakiram dauke da wuka inda ya nemi Morado ya nemi afuwansa, a nan suka fara cacar baki, nan take Samuel ya luma ma Morado wukar nan a kirji da ciki.” Inji Yansanda.

Daga karshe makwabta ne suka kira Yansanda, wanda suka kamo Samuel bayan ya boye a cikin dakin girke girke na gidan Morado, a yanzu dai yana can yana dana-sanin abinda ya aikata a hannun hukuma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel