Ka Dakatar da Shi': Gwamna ga Tinubu kan Zargin Dan Uwansa da Shirin Ta da Husuma

Ka Dakatar da Shi': Gwamna ga Tinubu kan Zargin Dan Uwansa da Shirin Ta da Husuma

  • Gwamna Ademola Adeleke ya zargi tsohon gwamna Adegboyega Oyetola da shirin tayar da zaune tsaye a Jihar Osun
  • Gwamnan ya yi wannan zargi ne a cikin wata inda ya ce Ministan ya shirya kawo rigimar daga ranar Litinin mai zuwa
  • Adeleke ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Oyetola, wanda ya kira ɗan uwansa, daga aiwatar da umarnin kotu da ke tayar da rikici
  • Ya kuma zargi Oyetola da haɗin baki da jami'an tsaro don hargitsa jihar, tare da jan kunnen cewa jama'a ba za su zauna lafiya ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Osogbo, Osun - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bukaci Bola Tinubu ya taka wa dan uwansa birki kan niyyar ta da husuma a jihar baki daya.

Gwamnan ya zargi minista, Adegboyega Oyetola da shirin tayar da zaune tsaye a jihar daga ranar Litinin 17 ga watan Janairun 2025 saboda buƙatar kansa.

Kara karanta wannan

'Ku bar sukar Tinubu': Malamin Musulunci kan tsadar rayuwa, ya kawo mafita ga yan kasa

Gwamna ya bukaci Tinubu ya taka wa ministansa birki
Gwamna Ademola Adeleke ya roki Tinubu ya dakatar da ministansa daga ta da husuma a Osun. Hoto: Ademola Adeleke, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gwamna ya roki Tinubu alfarma kan ministansa

Gwamnan ya yi wannan zargin ne a taron manema labarai ranar Lahadi 16 ga watan Janairun 2025, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adeleke ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Oyetola, wanda ya kira da ɗan uwansa saboda shirinsa na kawo tashin-tashina a jihar.

Gwamnan ya ce Oyetola na ƙoƙarin aiwatar da umarnin kotu da aka yi amfani da shi wajen dawo da shugabannin kananan hukumomi na jam'iyyar APC.

Gwamna ya shawarci al'ummar jiharsa su kare kansu

Ya ce jama'a za su kare kansu idan ba a dakatar da wannan yunƙurin neman mulki ba, TheCable ta ruwaito.

A cewarsa, Oyetola na haɗa baki da kwamishinan ‘yan sanda na jihar da daraktan DSS wajen tayar da tarzoma.

Ya ce:

"Na kira wannan taron ne don fallasa makarkashiyar tayar da rikici a Jihar Osun."

Gwamna ya daukaka kara kan rigimar sarauta

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

Kun ji cewa Gwamnatin Osun ta ce ta karɓi hukuncin kotu da mamaki, inda ta bukaci a zauna lafiya har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan rigimar sarauta.

Kwamishinan yada labarai a Osun, Kolapo Alimi, ya bukaci jami’an tsaro su tabbatar da zaman lafiya a garin Igbajo domin dakile matsalar tsaro da ka iya tashi.

Gwamnati ta gargadi al'umma da kada su dauki doka a hannunsu, domin hakan zai iya haddasa rikici a yankin da ma jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.