Rigima Ta Barke, Fusatattun Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin Yan Sanda Kurmus

Rigima Ta Barke, Fusatattun Masu Zanga Zanga Sun Kona Ofishin Yan Sanda Kurmus

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa zanga-zanga ta barke a jihar Ondo wanda ya yi sanadin asarar dukiyoyi
  • An ce matasa sun kona ofishin 'yan sanda a Ifon bayan mutuwar wani yaro da ake zargin an azabtar da shi a tsare
  • An tabbatar cewa wani abokin mamacin yana kwance a asibiti cikin mawuyacin hali, wanda ya jawo matasan suka fara bore
  • Kwamishinan 'yan sanda na Ondo, Wilfred Afolabi, ya tafi Ifon don tabbatar da zaman lafiya da hana rikicin ya tsananta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Akure, Ondo - An zargi matasa da kona ofishin ‘yan sanda a Ifon, hedkwatar karamar hukumar Ose a jihar Ondo.

Rahotanni sun tabbatar cewa haka ya faru ne bayan mutuwar wani yaro a tsare da ake zargin an azabtar da shi wanda ya yi sanadinsa.

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

Masu zanga-zanga sun kona ofishin yan sanda
Matasa sun kona ofishin yan sanda a Ondo kan zargin mutuwar yaro a hannunsu. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Akwai barazanar tsaro a Kudu maso Yamma

Bayanai sun nuna cewa matasan sun kai harin ne bayan sun ji labarin mutuwar yaron, yayin da abokinsa yake kwance a asibiti, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari na zuwa ne yayin da hukumomi ke kara tsaurara tsaro a Ondo saboda fargabar hare-haren yan ta'adda.

Ana fargabar yankin Kudu maso Yamma ka iya fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci bayan samun bayanan sirri.

A karshen watan Disambar 2024, Jami’an hukumar taro ta DSS sun kama mutanen da ake zargin ƴan ta'addan Boko Haram ne a jihar Osun.

Jami'an na DSS sun cafke mutanen guda 10 ne ake zargin mambobin Boko Haram ne a Ilesa da ke jihar.

Kwamishinan yan sanda ya shirya dakile matsalar

Kwamishinan 'yan sanda na Ondo, Wilfred Afolabi, ya tafi Ifon don kwantar da tarzomar da dakile rikicin yaduwa zuwa sassan yankin.

Kara karanta wannan

An yi kare jini biri jini tsakanin Boko Haram da ISWAP, da dama sun mutu

An tabbatar da cewa bayan kona ofishin yan sandan, wani gini da ke wurin shi ma an yi asararsa yayin zanga-zangar.

Mutane 30 sun mutu a hatsarin mota

Kun ji cewa mummunan hatsarin mota ya ritsa da fasinjoji da dama a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Majiyoyi sun ce hatsarin motan wanda ya ritsa da wasu motocin haya guda biyu, ya jawo asarar rayukan aƙalla mutane har guda 30.

Hukumar kiyayye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo, ta tabbatar da cewa hatsarin ya auku ne bayan motocin guda biyu sun yi karo da juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.