Tinubu Ya Manta da Sukar da El Rufai Ke Yi Masa, Ya Tura Masa Muhimmin Sako

Tinubu Ya Manta da Sukar da El Rufai Ke Yi Masa, Ya Tura Masa Muhimmin Sako

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ajiye bambancin da ke tsakaninsa da Malam Nasir El-Rufai, a gefe guda
  • Mai girma Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan na jihar Kaduna murnar cika shekara 65 a duniya
  • Shugaban ƙasan ya yaba da irin gudunmawar da El-Rufai ya ba da wajen kafa jam'iyyar APC da samun nasarorin ta a zabuƙan 2015, 2019 da 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, murnar cika shekaru 65 a duniya.

Shugaba Tinubu ya bayyana Nasir El-Rufai a matsayin malami, ɗan siyasa wanda da aka san shi da hazaƙa da basira.

Tinubu ya taya El-Rufai murnar cika shekara 65
Tinubu ya taya El-Rufai ya taya El-Rufai murna Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa wacce hadimin Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar wacce Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan takaddamar filin BUK, ya aika sako ga Gwamna Abba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya taya El-Rufai murna

An fitar da sanarwar taya El-Rufai murnar cika shekara 65 a duniya ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairun 2025.

Tinubu ya yaba da rawar da El-Rufai ya taka a wajen kafa jam'iyyar APC da kuma gudummawarsa wajen nasarar jam'iyyar a zaɓukan 2015, 2019, da 2023.

Shugaban ƙasan ya nuna godiya ga El-Rufai bisa ga ƙoƙarinsa wajen tabbatar da dimokuradiyya, hidimarsa ga ƙasa, da kuma yi wa matasa jagoranci.

Tinubu ya yi masa fatan ci gaba da samun lafiya da ƙarfin gwiwar ci gaba da hidimtawa ƙasar nan.

Tinubu ya ƙwararo yabo ga El-Rufai

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mallam Nasir Ahmad murnar cika shekara 65 a duniya."
Mallam El-Rufai shugaba ne, malami kuma ɗan siyasa. Yana ɗaya daga mutanen da suka kafa jam'iyyar APC, kuma ana ganin ƙimarsa saboda hazaƙa da basirarsa."
 "Ya yi gwamnan jihar Kaduna na tsawon shekara takwas, kuma kafin a zaɓe shi, ya riƙe muƙamin shugaban hukumar BPE da ministan birnin tarayya Abuja daga shekarar 2003 zuwa 2007."

Kara karanta wannan

"Na ɗauke shi uba," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa jagoran Yarbawa rasuwa

"Shugaba Tinubu ya Mallam El-Rufai murna a wannan lokaci sannan ya yaba da ƙoƙarin da yake yi kan dimokuraɗiyya, hidimtawa ƙasa da ɗora matasa a kan hanya."
"Shugaba Tinubu ya na yi wa El-Rufai fatan lafiya da ƙwarin gwiwar ci gaba da hidimtawa ƙasar nan."

- Bayo Onanuga

El-Rufai ya samu goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya samu goyon bayan daga ƙungiyar kare haƙƙin musulmi wato MURIC.

Ƙungiyar MURIC ta ja kunnen gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da ka da ta tozarta tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng