Sabon Salo: ’Yan Fashi Sun Shiga Har Cikin Jami’a, Sun Yi Dalibai Fashin Kayan Alatu

Sabon Salo: ’Yan Fashi Sun Shiga Har Cikin Jami’a, Sun Yi Dalibai Fashin Kayan Alatu

  • ‘Yan fashi sun kutsa har cikin jami’a tare da aikata sata, sun dauke wayoyi da kayan alatun dalibai a dakin kwana
  • ‘Yan sanda sun gaggauta kawo dauki, inda a halin yanzu wasu daga cikin ‘yan fashin ke hannu, ana ci gaba da bincike
  • Jami’ar da ‘yan sanda sun bayyana matakin da suke dauka domin kaucewa aukuwar irin wannan lamari a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ibadan, jihar Oyo - Wasu ‘yan fashi sun mamaye Awolowo Hall da ke Jami’ar Ibadan, Jihar Oyo, a daren ranar Asabar, inda suka wawashe kayayyakin dalibai na daruruwan Naira.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan fashin sun kwashe wayoyi masu tsada, kayan ado, tufafi, da sauran kayayyaki masu daraja mallakin daliban.

Har ila yau, an ce wasu dalibai sun ji rauni sakamakon tsoratarwa da cin zarafin da ‘yan fashin suka yi masu yayin harin, rahoton jaridar Leadership.

Yadda aka yiwa dalibai sata a jami'a
An yiwa dalibai sata a jami'ar Ibadan | Hoto: ui.edu.ng
Asali: UGC

Yadda ‘yan fashi suka kutsa jami’a

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

Shaidu sun bayyana cewa ‘yan fashin sun kutsa cikin dakin daliban ne da misalin karfe biyu na dare, inda suka far masu ba tare da wata fargaba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa, sun shigo ne kiƙe makamai irin su wuka da sanda, sannan suka tilasta wa daliban mika musu kayansu masu daraja.

Wata majiya daga jami’ar ta ce jami’an tsaro sun samu kiran gaggawa daga daliban da abin ya shafa, inda suka yi sauri suka je wurin da abin ya faru, amma kafin isowarsu, ‘yan fashin sun riga sun yi awon gaba da kayayyakin da suka kwasa.

Daukin da ‘yan sanda suka kawo

A yayin da ‘yan sanda suka isa wurin, sun kama wasu daga cikin ‘yan fashin, sannan suka mika su ga ofishin ‘yan sanda na Sango domin ci gaba da bincike.

Hukumar jami’ar ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin gano yadda harin ya faru da kuma yadda aka samu shigar barayin cikin jami'a.

Kara karanta wannan

"Muna lalata da sama da maza 12 a rana": An ji ta bakin 'yan mata da ke karuwanci

A halin yanzu, ana ci gaba da farautar sauran ‘yan fashin da suka tsere daga wurin domin gurfanar da su gaban doka.

Matakin da ‘yan sanda ke dauka yanzu

Rundunar ‘yan sanda ta ce ba za ta kyale irin wannan laifi ya ci gaba da faruwa ba, kuma ana cigaba da binciken yadda ‘yan fashin suka samu damar kutsawa cikin jami’ar, Tribune Online ta ruwaito.

Kakakin Jami’ar Ibadan, Misis Joke Akinpelu, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa rahotannin da aka samu daga masu kula da daliban sun nuna cewa ‘yan fashin sun kwashe wayoyi da sauran kayayyaki masu daraja na daliban.

Ta kuma bayyana cewa jami’ar za ta kara matakan tsaro domin kare lafiyar dalibai daga irin wannan farmaki nan gaba.

Abin da dalibai suka sani game da barnar

Wani dalibi da abin ya shafa, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya ce abin ya tayar masu da hankali matuka:

Kara karanta wannan

Sojoji sun raunata 'yan sanda yayin da suka daku da juna, an ladabtar da jami'ai

A cewarsa:

“Mun firgita sosai, ba mu san me za mu yi ba. Sun zo cikin dare suka dinga dukan kofarmu, sannan suka shiga suka tilasta mana ba su wayoyinmu da sauran kayayyakinmu.”

Jami’an tsaro sun bukaci al’umma da su kai rahoto kan duk wani mutum da suke zargi da hannu a harin domin a kama su a hukunta su.

Haka kuma an bukaci dalibai su kasance masu kula da juna tare da bin matakan tsaro da jami’ar ke bayarwa domin rage yawaitar irin wannan hari a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel