Tsagwaron Son Zuciya Ya Sa Malamin Addini Kashe Dalibar da Ya Hadu da Ita a Facebook
- An kama wani mai ikrarin malunta da kisan wata budurwa da ya hadu da ita a Shafin Facebook a wani yankin jihar Kwara
- ‘Yan sanda sun bayyana yadda mutumin ya yi datsa-datsa da sassan jikinta da sunan yin tsafi, lamarin da ya tada hankali
- Ba wannan ne karon farko da ya aikata wannan laifin ba, alamu sun nuna ya taba aikata irin wannan mummunan aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ilorin, jihar Kwara - An kama wani mutum mai ikirarin malunta, AbdulRahman Bello, a garin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, bisa zargin kashe wata daliba domin ya yi tsafi da ita.
Marigayiyar mai suna Hafsoh Lawal Yetunde, daliba ce a shekarar karshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ke Ilọrin.

Asali: Facebook
Rahotanni sun bayyana cewa, an rasa inda take tun ranar 10 ga Fabrairu, 2025, bayan ta halarci wani bikin suna, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda ya kawo ta gidansa, ya hallaka ta
Shaidu sun ce yayin da take cin abinci a gidan suna, sai ta amsa kira daga wayarta sannan ta fice daga gidan, daga nan kuma ba a sake jin duriyarta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargi ya hadu da ita ne a shafin Facebook, inda ya yi amfani da wata dabara ya samu lambar wayarta sannan ya gayyace ta zuwa gidansa.
Da iyayenta suka ga shiru, sai suka garzaya ofishin ‘yan sanda na Oja-Oba a Ilorin domin kai rahoto kan bacewar ‘yarsu.
Yadda ya amsa laifin kashe budurwa
Majiyoyi sun ce bayan da aka kai rahoton batan nata, ‘yan sanda sun bi diddigin lambar wayarta kuma suka gano cewa kiran karshe da ta yi ya kasance ne ga wanda ake zargi da ke Offa, ko da yake gidan iyayensa yana Isalekoto.
Da aka kama shi, da farko ya musanta sanin inda take, amma bayan da aka binciki gidansa, sai ya amsa cewa ta zo wajensa amma ta mutu sakamakon tashin cutarta ta asthma.
Bincike ya bankado wata tukunya mai dauke da sassan jikinta tare da wasu kayan aikin da aka yi amfani da su wajen yankata ta, Punch ta ruwaito.
Ya saba aikata barnar kisan kai
Rahotanni sun ce wasu kayan da aka gano a gidansa sun nuna cewa ba wannan ne karo na farko da yake aikata irin wannan aika-aika ba, domin kuwa an tarar da wani tebur da ke dauke da kayan yanka.
An kuma bayyana cewa wanda ake zargin yana da alaka ta jini da wani babban malamin addini daga yankin Isalekoto wanda ya rasu kwanan nan.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya bayyana wannan al’amari a matsayin abu mai ta da hankali.
An kashe daliba a kwaleji
A wani labarin na daban, an kashe wata dalibar kwaljin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).
Jaridar 21st CENTURY CHRONICLE ta ruwaito cewa an kashe dalibar Deborah ce bayan an bukaci ta janye kalamanta na batanci amma ta ki.
Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe, lamarin da daga baya ya jawo cece-kuce.
Asali: Legit.ng