Yadda aka kashe ‘Dalibar da ke karatun Likitanci a Jami’ar da ke Zariya
- Kwanaki ‘Yan Sanda su ka damke wanda ake zargi da kashe wata ‘Daliba
- Wani ‘Dan acaba ne ya kashe wata ‘Daliba da ke ajin farko a Jami’ar ABU
- Yanzu Jami’an Jami’ar sun tsaurara matakai na yawo a cikin Makarantar
Mun samu labari yadda aka kashe wata ‘Dalibar likitancin dabbobi da ke ajin farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Garin Zariya. Yanzu haka dai idan ba ku manta ba tuni Jami’an tsaro sun yi nisa da bincike.
Legit.ng ta yi hira da ‘Yan acaba a Samaru inda wannan abu ya faru makon nan wanda su ka bayyana mana cewa wani Bawan Allah ne ya dauki wasu ‘Dalibai mata 2 a babur domin ya kai su wata Unguwa da Ma’aikatan A.B.U ke zama.
KU KARANTA: Wani mutumi ya aika mai dakin sa har lahira
Wannan unguwa dai tana gaba da asalin sashen Jami’ar ne inda bayan an yi nisa ne wannan mai babur ya nemi fisge wayoyin salular wannan ‘Daliba. Kafin nan dama ya ajiye ‘yar uwar ta a hanya kamar yadda rahoton ya zo mana.
A nan ne fa wannan mutumi ya bugi wannan ‘Daliba har tace ga garin ku nan. An dai dace an yi ram da daya daga cikin masu laifin bayan ya tafi da wayoyin wannan yarinya. Yanzu haka dai Jami’ar ta tsaurara matakai na babur.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng