Sowore: 'Yan Daba Sun Kai Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Hari, An Ji Musu Raunuka

Sowore: 'Yan Daba Sun Kai Wa Dan Takarar Shugaban Kasa Hari, An Ji Musu Raunuka

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, hari a garin Lagos
  • Sowore da ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC ya gamu da iftila'in ne a yau Asabar yayin gasar tsere
  • ‘Yan daba sun kai wa Sowore da ma’aikatan kafar sadarwarsa hari yayin da suke halartar gasar, sun kuma ji wa ‘yan jarida rauni
  • Wasu a cikin wani bidiyo sun nuna yadda aka cakwamo wani ɗan jarida daga wuya yayin da yake riƙe da abin daukar hoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ikeja, Lagos - Rahotanni da muke samu sun ce an kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Omoyele Sowore hari.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 15 ga watan Janairun 2025 yayin gasar 'Lagos City Marathon'.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun firgita da cewa 'Allah ya yi wahayi' makiyaya za su kai hari

An kai farmaki kan tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya
Yan daba sun farmaki tsohon dan takarar shugaban kasa. Hoto: Omoyele Sowore.
Asali: Twitter

Abin da Yele Sowore ya ce kan belinsa

Punch ta ce an kai wa Sowore da ya yi takara karkarshin jam'iyyar AAC hari tare da ma’aikatan kafar sadarwarsa yayin da suke halartar gasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan zargin Sowore a yan kwanakin nan da cin zarafin wasu jami'in tsaro ta yanar gizo.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce ba zai yarda shugaba Bola Tinubu ya tsaya masa a harkar beli ba.

Bayan gurfanar da shi a kotu, ya ƙi amincewa da sharuɗan beli da suka haɗa da mika fasfo dinsa da samar da babban ma’aikacin gwamnati.

Wasu yan daba sun farmaki Sowore a Lagos

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan daban sun ji wa ‘yan jarida da dama rauni tare da lalata musu kayan aiki, cewar rahoton PM News.

A cikin bidiyon da aka yada, an ga ‘yan daban na dukan Sowore, ma’aikatansa da kuma ‘yan jaridar, an lalata kamara da sauran kayan aikin su.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

An dura kan Sowore bayan sukar Buhari

A baya, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya tunzura wasu ƴan Najeriya kan kalaman da ya yi a kan Muhammadu Buhari.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya yi kalamai masu kaushi a kan Buhari inda ya zarge shi da lalata ƙasar Najeriya.

Sai dai, kalaman da Sowore ya yi a kan Buhari, sun jawo masa suka daga wasu ƴan Najeriya waɗanda ba su ji daɗinsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.