Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Laifin da Tinubu Ya Yi Wa Manyan Arewa
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bayyana yadda wasu ƴan Arewa suke jinkan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Ismaeel Ahmed ya bayyana cewa wasu manyan Arewa na jin cewa Shugaban kasa Tinubu ya mayar da su saniyar ware
- 'Dan siyasar ya ce suna jin hakan ne bayan ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da cewa ya samu ƙuri'u a yankin a zaɓen 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban matasa na APC, Ismael Ahmed, ya yi magana kan laifin da shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu manyan Arewa.
Tsohon hadimin na Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan Arewa na jin an ware su daga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Facebook
Ismaeel Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels tv a shirinsu na 'Inside Sources'.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ware wasu manyan yankin Arewa
Ya ce manyan Arewan na jin an ware su ne duk da irin rawar da suka taka wajen samar masa da ƙuri'u a zaɓen 2023.
"Mutane da dama daga Arewa sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da cewa Tinubu ya lashe zaɓe."
"Akwai Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso da suka tsaya takara, dukkansu ƴan siyasar Arewa ne, amma duk da haka Tinubu ya lashe jihohi huɗu a Arewa ta Tsakiya, uku a Arewa ta Yamma, daya a Arewa ta Gabas, inda ya samu ƙuri’u masu yawa."
“A jihar Kano kadai mun ba Tinubu sama da ƙuri’u 500,000. Amma yanzu ƴan Arewa na tambaya ‘shin muna da cikakken wakilci a wannan gwamnati?’"
- Ismaeel Ahmed
Ismael Ahmed ya ce ko da shugaban ƙasan zai fitar da jerin sunayen muƙaman ya naɗa, wasu daga cikin manyan Arewa na jin an ware su, wanda hakan ke ƙara shafar talakawan yankin.

Kara karanta wannan
Shugaban Binance ya buɗe baki, ya jero sunayen ƴan Majalisa 3 da suka nemi cin hanci
Ya kuma ce mutanen yankin Kudu maso Gabas na jin hakan, amma ba su da ƙarfi kamar na Arewa saboda ba su kaɗawa Tinubu ƙuri’u kamar ƴan Arewa ba.
Tsohon hadimin Buhari ya ba Tinubu shawara
Tsohon mai ba da shawarar ya buƙaci Tinubu da ya tabbatar da cewa dukkanin yankunan ƙasar nan na jin ana damawa da su, domin ya zama shugaban ƙasa na kowa da kowa.
“Ina ganin shugaban ƙasa yana iya ƙoƙarinsa, amma akwai buƙatar ya ƙara zage damtse. Na yi tsammanin ya zuwa yanzu ya kamata ya kai ziyara a wasu jihohi a faɗin ƙasar nan, ba wai kawai don ƙaddamar da ayyuka ba, amma don jin ra’ayoyin jama’a."
“Kano kaɗai tana da 10% na yawan al’ummar Najeriya. Ya kamata shugaban ƙasa ya kai ziyara a Kano, ko da kuwa ba don siyasa ba ne. Na ga ya ziyarci Enugu, hakan na da kyau, amma ina ganin ya kamata ya ziyarci wasu yankuna da dama."
"Ya kamata ya buɗe ƙofofin da za a riƙa samunsa. Mutane na bukatar su san cewa wakilansu na da damar shiga wurin shugaban ƙasa domin bayyana matsalolinsu."
- Ismael Ahmed
Kwankwaso ya ce Tinubu zai samu ƙuri'u a Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC ta jihar Kano, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa Shugaba Bola.Tinubu zai samu ƙuri'u a Arewacin Najeriya.
Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa dattawan Arewa ba su isa su sanya shugaban ƙasan ya ƙi samun ƙuri'u ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng