Magana Ta Fara Fitowa kan Zargin Ƴan Majalisa 3 da Neman Cin Hancin $150m daga Binance

Magana Ta Fara Fitowa kan Zargin Ƴan Majalisa 3 da Neman Cin Hancin $150m daga Binance

  • Mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Philip Agbese ya musanta hannu a zargin neman cin hanci daga wani jami'in Binance
  • Ya ce Tigran Gambaryan karya yake masa kuma ya ba jami'in kamfanin crypto wa'adin kwana bakwai ya janye kalamansa ko da ya bada hujja
  • Hon. Agbese ya ce akwai lokacin da ya kai ziyara ofishin Hon. Peter Akpanke ya tarar suna tattaunawa da wakilan Binance amma bai san komai ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mataimakin mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Hon. Philip Agbese, ya musanta zargin cewa ya nemi cin hanci daga jami’in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan.

A cewarsa, zargin da Gambaryan, jami'in kamfanin hada-hadar kuɗin crypto watau Binance, ya yi ba shi da tushe balle makama.

Hon. Philip Agbese.
Hon. Philip Agbese ya musanta zargin karɓar cin hanci daga Binance Hoto: Hon. Philip Agbese
Asali: Facebook

Hon Agbese ya bai wa jami’in Binance ɗin wa’adin kwana bakwai ya gabatar da hujja kan zargin sun nemi cin hanci ko kuma ya janye maganarsa, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an Binance ya faɗi ƴan Majalisa 3

Gambaryan ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan majalisa guda uku, Philip Agbese, Peter Akpanke, da Ginger Obinna Onwusibe, sun nemi cin hancin Dala miliyan 150 daga hannunsa.

Ya ce ƴan Majalisar sun zo sun gana shi a lokacin da ake tsare da shi a Najeriya a shekarar 2024, inda aka tuhume shi da zamba.

Kakakin Majalisa ya ƙaryata Gambaryan

A cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken: “Binance: Kawo shaida ko ka fuskanci hukunci," Agbese ya musanta zargin yana da hannu a tattaunawa da jami’an Binance

Hon. Agbese ya ce:

"Na fusata matuka da wannan ƙarya da Tigran Gambaryan ya yi, yana ikirarin cewa ni da wasu ‘yan majalisa mun bukaci cin hanci daga gare shi.
"Ba ni da wata alaƙa da kwamitin da ke binciken laifukan da suka shafi kudi. Na ziyarci abokina, Hon. Peter Akpanke, a ofishinsa inda yake ganawa da wasu baƙi dangane da aikinsa a kwamitin da yake jagoranta.

Kara karanta wannan

Shugaban Binance ya buɗe baki, ya jero sunayen ƴan Majalisa 3 da suka nemi cin hanci

"Mun gaisa, kuma mun tattauna a kan wasu batutuwa da suka shafi kamfanin Binance, amma ba tare da wata bukata ta kudi ba."

"Ba ni da asusun cryto" - Philip Agbese

Hon. Agbese ya ce bai taɓa yin hulɗa da kamfanin Binance ko amfani da kuɗin crypto ba, kuma bai da asusun ajiyar crypto a ko’ina a duniya.

Ya kuma bukaci Gambaryan ya mayar da hankali kan shari’ar da ke gabansa a hukumar EFCC, maimakon ya nemi guduwa daga laifin da ake tuhumarsa da shi.

Hon. Philip Agbese ya bayyana cewa a lokacin da ya kai ziyara ofishin Hon. Peter Akpanke, ya tarar da Hon. Peter Anekwe a wurin.

Agbese ya bayyana gaskiyar abin da ya faru

Ya ce a lokacin an shaida masa cewa suna tattaunawa da tawagar Binance daga ƙasashen waje dangane da wani al'amari da aka gabatar wa kwamitinsu.

Ɗan Majalisar ya ƙara da cewa bayan ya bar ofishin, bai san abin da ya faru tsakanin su da jami’an Binance ba, kuma bai sake ganin baƙin ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Dan majalisa ya hada Ganduje da El Rufa'i, ya gyara musu zama kan 2027

Haka kuma, ya jaddada cewa bai taɓa halartar wata tattaunawa da Binance, EFCC ko DSS ba bayan wannan gajeriyar ganawa.

Wannan bayani na nufin yana nesanta kansa daga duk wani zargi na cin hanci da aka danganta da shi, yana mai cewa idan wani abu ya faru da Binance bayan barinsa ofishin, ba shi da masaniya a kai.

Dalilin ƙara N700bn a kasafin kudin 2025

A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar wakilai, Abubakar Kabiru Abubakar Bichi ya ce an ƙara N700bn a kasafin 2025 ne saboda janye tallafin da Amurka ta yi.

Hon. Abubakar Bichi, wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi ya ce Amurka ta janye tallafin da take ba Najeriya a ɓangaren lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel