Shugaban Binance Ya Buɗe Baki, Ya Jero Sunayen Ƴan Majalisa 3 da Suka Nemi Cin Hanci
- Shugaban Binance da aka tsare kwanakin baya a Najeriya, Tigran Gambaryan ya yi zargin cewa ƴan Majalisa uku sun nemi cin hanci a wurinsa
- Gambaryan ya bayyana cewa ƴan Majalisar tarayyan sun gana da shi, suka nemi ya tura masu Dala miliyan 150 a asusun ajiyarsu na sirri
- Duk da ya ce ya manta sunan ɗaya daga cikinsu amma ya bayyana sunayen ƴan Majalisa biyu da suka zo wurinsa bisa umarnin wani takwaransu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tigran Gambaryan, shugaban sashen binciken laifukan kudi na kamfanin hada-hadar kudaden crypto watau Binance, ya yi magana kan ƴan Majalisar da suka nemi cin hanci.
Gambaryan ya bayyana sunayen wasu ‘yan majalisar dokokin Najeriya uku da ya ce sun nemi cin hancin dala miliyan 150 ($150m) daga gare shi lokacin da yake tsare.

Asali: Twitter
Shugaban Binance, wanda ya kwashe watanni yana tsare a Najeriya, ya jero sunayen a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen ƴan Majalisa 3 da ya ambata
Sunayen 'yan majalisar da Gambaryan ya ambata su ne:
1. Peter Akpanke
2. Philip Agbese (mataimakin kakakin majalisa wakilai)
3. Ginger Obinna Onwusibe (shugaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa)
A saƙon da ya fitar, shugaban Binance din ya ce Peter Akpanke da Philip Agbese sun zo wurinsa tare da wani ɗan Majalisa da ya manta sunansa.
Ya kuma ƙara da cewa sun zo bisa umarnin Ginger Obinna Onwusibe, inda suka nemi ya biya cin hancin Dala miliyam 150.
Yadda ya gana da ƴan Majalisar Wakilai
Gambaryan ya ce a ranar 5 ga watan Janairu, 2024, jami’an hukumar DSS suka bukace shi da ya gana da majalisar wakilai kafin su yanke hukunci a kansa.
A cewarsa, lokacin da ya gana da ’yan majalisar guda uku, sun nemi ya bi abin da suke so daga karshe suka bukaci a biya su cin hanci a kudin crypto zuwa asusun ajiyarsu na sirri.
“Sun kafa kyamarori don yin kamar taron na gaske ne, amma ko da kyamarorin ba a haɗa su da wuta ba. A ƙarshe, sun bukaci dala miliyan 150 a matsayin cin hanci,” in ji Gambaryan.
Majalisa ta musanta zargin a wancan karon
Lokacin da aka yaɗa jita-tar wannan batu a wancan lokacin, majalisar wakilai ta ta fito musanta cewa wani mambanta ya nemi cin hanci daga Binance.
A halin yanzu dai bayan ikirarin da Gambaryan ya yi, ana sa ran wadanda aka ambata za su mayar da martani kan wannan sabon zargi.
Binance ya cire Naira a harkokinsa
Ku na da labarin, kamfanin hada-hadar kudin crypto watau Binance ya dakatar da duk wata hada-hada ta shafi kuɗin Najeriya watau Naira.
Wannan mataki ya biyo bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na kama wasu jami'an Binance guda biyu, ta ce tana zargin kamfanin da taimakawa wajen hada-hadar kudin haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng