Birkin Tirela Ya Tsinke a Kano, Ta Murkushe Mutane da Dama
- Rahotanni na nuni da cewa wani hadari mai muni ya auku a gadar Muhammadu Buhari da ke Kano yayin da birkin tirela ya tsinke
- Bayanan da aka samu sun tabbatar da cewa an samu mace-mace da raunuka masu tsanani sakamakon hatsarin babbar motar
- Hukumar kashe gobara ta Kano ta cewa manema labarai tana ci gaba da kokarin tattara cikakkun bayanai game da lamarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Wani mummunan hadari ya auku a gadar Muhammadu Buhari a Kano, inda wata tirela ta rasa birki, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da dama yayin da wasu suka jikkata.
Rahotanni sun bayyana cewa tirelar tana kan hanyarta ta zuwa Kudancin Najeriya ne a lokacin da ta kubuce, ta fada cikin wata rami a karkashin gadar.

Kara karanta wannan
'Suna jawo bala'i': Basarake ya haramta ayyukan bokaye mata bayan kisan dan majalisa

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa har yanzu ba a gama tattara bayanai kan barnar da motar ta yi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan hatsari ya faru a wurin ba, inda a cikin shekara guda an samu haduran da suka hada da rasa rayuka da jikkata mutane.
Yadda hatsarin tirela ya faru a Kano
Wani shaidar gani da ido, Shu’aibu Hamisu, ya ce tirelar na tahowa ne daga titin Maiduguri lokacin da ta kubuce tana kokarin shiga karkashin gadar ta hanyar da ke hade da titin Zariya.
A cewar Shu’aibu Hamisu:
"Tirelar ta zame cikin ramin da ke karkashin gadar. An samu wadanda suka tsira da ransu, amma da yawa sun mutu nan take,"
Wani mai amfani da shafukan sada zumunta, Yahya Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:
"Tirelar ta kife a Hotoro NNPC, tana dauke da mutane da kaya. Hadarin ya afka ga fiye da mutum 20 wasu sun rasu, wasu kuma sun ji munanan raunuka."
Yawan hadarin tirela a jihar Kano
Rahotanni sun bayyana cewa wannan wuri yana daga cikin wuraren da ake fama da haduran manyan motoci a Kano, musamman ma tirelolin da ke tahowa daga Arewa zuwa Kudu.
Wani mai sana’a da ke yankin ya ce:
"A mafi yawan lokuta, direbobi na kin yin taka-tsantsan a wannan wuri. Suna yawan tunanin cewa za su iya ratsawa cikin sauri, wanda hakan ke janyo hadura."
Hukuma tana tattara bayanai game da hadarin
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa suna kan kokarin tattara cikakkun bayanai kan hadarin.
An bukaci direbobi da su rika kiyaye dokokin tuki, musamman a wuraren da suka san suna da hadari, domin gujewa afkuwar irin wadannan munanan hadura.
Tankar mai ta yi hadari a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa an samu hadarin tankar man fetur a wani gidan mai a birnin Dutse na jihar Jigawa.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa an yi nasarar kammala kashe wutar ba tare da asarar rai ko daya ba sai dai dukiya da aka rasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng