Auren Ƴar Majalisa Ya Gamu da Tangarɗa, Mahaifiyar 2baba Ta Saki Sabon Bidiyo
- Mahaifiyar fitaccen mawakin nan, 2baba ta kawo tangarɗa a shirinsa na auren ƴar Majalisar dokokin Edo, Hon. Natasha Osawaru
- A wani bidiyo da ya fara yawo a soshiyal midiya, mahaifiyar 2baba ta roki ƴar Majalisa ta rabu da ɗanta saboda ba ya cikin hankalinsa
- Ta ce ɗanta yana cikin ruɗani da takaicin rabuwa da tsohuwar matarsa, don haka ta roki ƴar Majalisar ta haƙura da batun auren da ya kawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Mahaifiyar shahararren mawaki, Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2baba ko 2face, ta roƙi ƴar Majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Natasha Osawaru ta rabu da ɗanta.
Mafaifiyar fitaccen mawakin a Najeriya ta buƙaci ƴan uwanta iyaye mata na faɗin ƙasar nan su taya ta rokon ƴan Majalisar ta haƙura da batun auren ɗanta watau 2baba.

Asali: Instagram
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin ƴan uwan 2baba na Instagram ranar Alhamis, Mrs. Rose Idibia ta bayyana damuwarta kan soyayyar danta da ‘yar majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da mahaifiyar 2Baba take buƙata
Ta bayyana cewa danta yana cikin damuwa da rudani saboda shirin rabuwa da tsohuwar matarsa, Annie Macaulay-Idibia, kuma hakan na iya shafar hankalinsa.
“'Yan Najeriya barka da yamma. Ni ce Mrs. Rose Idibia, mahaifiyar 2face, wannan saƙo ne zuwa ga Miss Natasha Osawaru ta Edo. Ina roƙon iyaye mata su taimake ni su roƙe ta ta bar min ɗana.
"Ɗana yana cikin ruɗanin rabuwa da matarsa, kuma ba a cikin hankalinsa yake ba a yanzu. Na san ɗana sosai, wannan ba shi ba ne.
"Natasha, zan roƙe ki, ki cire mundaye da zobukan da kika daura masa, ki bar shi ki rabu da shi,” in ji mahaifiyar 2baba wacce tana magana tana kuka.
Soyayyar 2Baba da ƴar majalisar Edo
Rahotanni sun nuna cewa 2Baba ya yiwa Natasha tayin aure a wani taro, inda ya gabatar tare da sanya mata zobe a gaban wasu abokansa.
Wannan matakin ya biyo bayan raba gari da Annie Idibia, wadda ya kasance da ita a matsayin mata na tsawon shekaru.
Tun da farko, mutane sun fara zargin akwai soyayya tsakanin mawakin da Natasha bayan da aka gansu tare a Majalisar dokokin jihar Edo da kuma wani kulob a Legas.
Lamarin dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayan sabuwar soyayyar 2baba, yayin da wasu ke nuna damuwa kan halin da Annie ke ciki.
To sai dai a yanzu bayan soyayyar ta yi karfi har an sa zoɓe, alamun shirin aure, mahaifiyar mawakin ta fara kawo tangarɗa.
2baba ya nemi auren Hon. Natasha
A baya, kun ji cewa fitaccen mawakin ya sanya wa ƴar majalisar dokokin jihar Edo, Hon. Natsaha zoben neman aurenta a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan
Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana
Bidiyon dai ya nuna cewa Natasha ta amince da auren 2baba bayan ta karɓi zoben da ƴa ba ta, lamarin da ya haddasa maganganu a soshiyal midiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng