Rikicin Sarauta: Gwamna Ya Ɗaukaka Ƙara, Kotu Ta Bar Mai Martaba Sarki kan Mulki
- Babbar kotun jihar Kogi ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ya tsige Sarkin Ebira, Mai martaba Ahmed Anaje daga kan sarauta
- Mai shari'a Umar Salisu ya ba da umarnin kowa ya tsaya a matsayinsa bayan gwamnatin Kogi da mai martaba sarkin sun shigar da ƙara
- A ranar 3 ga watan Fabrairu, 2025, kotun ta sauke basaraken daga mulki a wata ƙara da mutane uku suka shigar suna kalubalantar naɗinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi - Babbar Kotun jihar Kogi da ke Lokoja ta maido da sarkin kasar Ebira watau Ohinoyi, Alhaji Ahmed Muhammed Anaje kan karagar mulki.
Kotun ta umarci a tsaya a matsayin da ake, ma'ana sarkin ya ci gaba da zama a kan karagarsa har sai an kammala shari'a.

Asali: Twitter
Tribune Nigeria ta tattaro cewa mai shari’a Umar Salisu na Kotun VI ya bayar da wannan umarni bayan da masu kara suka nemi dakatar da aiwatar da hukuncin da ya tsige sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaddda kotu ta tsige sarkin Ebira a Kogi
A ranar 3 ga watan Fabrairu, 2025 Mai Shari'a Salisu ya tsige Ahmed Anaje daga sarautar sarkin Ebira bisa hujjar cewa an saɓa doka wajen naɗinsa.
Alkalin ya yanke wannan hukunci ne a shari'ar da wasu mutun uku, Daudu Adeku-Ojiah, Hussain Yusuf, da Abdulrahaam Suberu suka shigar gabansa.
Masu karar sun kalubalanci nadin da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya yi wa Mai Martaba Ahmed Anaje.
Gwamna Ahmed Ododo ya ɗaukaka ƙara
Da yake mayar da martani, Gwamna Ododo, da Atoni-Janar da Ohinoyi, sun ce sun shigar da kara kan hukuncin a gaban kotun daukaka kara suna kalubalantar hukuncin.
Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na Kogi, Muiz Abdullahi (SAN), tare da Ohinoyi, sun shigar da ƙorafi a gaban kotu, suna neman a dakatar da aiwatar da hukuncin.
Sun nemi a dakatar da hukunci ne saboda sun riga sun daukaka kara zuwa kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Kotu ta bar mai martaba sarki kan mulki
Da yake yanke hukunci kan bukatar gwamnatin Kogi da tsigaggen basaraken, Mai shari’a Salisu ya umarci kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yi hukunci.
Alkalin ya ce:
“Tun da masu ƙara sun bayyana cewa har yanzu akwai muhimman batutuwa da ke gaban wannan kotu da kotun daukaka kara, ya kamata a bar komai yadda yake har sai an yanke hukunci na ƙarshe.”
Rahoton The Guardian ya nuna wannan hukunci ya ba Ohinoyin Ebira damar ci gaba da zama a karagar mulki har sai an yanke hukuncin karshe.
Manyan sarakuna 5 da kotu ta tsige
A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku manyan sarakuna biyar masu daraja, waɗanda kotu ta tuɓewa rasawani bisa dalilai daban-daban cikin shekara ɗaya.
Ohinoyi na ƙasar Ebira na ɗaya daga cikinsu bayan kotu ta yanke hukuncin tsige shi daga sarauta saboda an saɓa doka da al'adun masarauta wajen naɗa shi a 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng