13 ga Fabrairu: Majalisar Wakilai Ta Karrama Tsohon Shugaban Ƙasa da Allah Ya Yi Wa Rasuwa

13 ga Fabrairu: Majalisar Wakilai Ta Karrama Tsohon Shugaban Ƙasa da Allah Ya Yi Wa Rasuwa

  • Majalisar Wakilai ta ƙasa ta sanya ranar 13 ga watan Fabrairun kowace shekara ta zama ranar tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammed
  • A zaman yau Alhamis, Majalisar ta yi shirun minti ɗaya domin karrama marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja wanda ya rasu a 1976
  • Bayan haka, Rt. Hon Tajudeen Abbas ya sanar da kafa sababbin kwamitoci biyu da waɗanda za su jagorance su don kawo ci gaba a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar Wakilai ta Najeriya a ranar Alhamis ta karrama tsohon shugaban mulkin soja, Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed.

Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa daga yanzu, Majalisar za ta riƙa bikin ranar 13 ga Fabrairu a matsayin ranar Murtala Muhammed don tunawa da marigayi tsohon shugaban ƙasar.

Majalisar Wakilai.
Majalisa ta karrama marigayi tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Muhammed Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

A yayin zaman yau Alhamis, Majalisar ta yi shiru na minti guda domin girmama shi, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Majalisa: "Matasa sama da 500,000 a jihohin Arewa 2 sun rasa aikin yi"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rayuwa da gwamnatin Murtala Muhammed

Marigayi Murtala Muhammed ya shugabanci Najeriya daga 1975 zuwa 1976, kafin a kashe shi a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

An kashe Murtala Muhammed ne a wani yunkurin juyin mulki da Laftanal Kanal Buka Suka Dimka ya jagoranta wanda bai samu nasara ba.

Bayan mutuwarsa, Janar Olusegun Obasanjo ya gaje shi, inda ya ci gaba da aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsarensa.

Murtala Muhammed na daya daga cikin shahararrun shugabanni a tarihin Najeriya, kuma ana girmama shi da abubuwa da dama ciki har da filin jirgin mama na Legas da aka raɗawa sunansa.

Sauye-sauye a kwamitocin Majalisa

A wani cigaba, Majalisar Wakilai ta ƙirƙiri sabbin kwamitoci guda biyu a zamanta na yau bayan karrama tsohon shugaban ƙasar.

1. Kwamitin kula da hukumar raya yankin Kudu maso Yamma – Majalisar ta naɗa Hon. Akin Adeyemi a matsayin shugaba, tare da mataimakinsa Hon. Clement Akani.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

2. Kwamitin kula da hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya – Majalisa ta naɗa Hon. Tunji Olawuyi a matsayin shugaba, tare da mataimakinsa Hon. Donald Ojogo.

Wadannan kwamitoci biyu sun ƙara yawan kwamitocin Majalisa, domin tabbatar da ci gaba a yankuna daban-daban na ƙasar nan, in ji Punch.

Majalisa ta amince da kasafin 2025

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta amince da kasafin kudin 2025 wanda shugaban kasa, Bola Tinubu ya gabatar.

Kasafin wanda zai laƙume sama da Naira tiriliyan 54 a 2025, ana sa ran zai maida hankali ne kan ayyukan more rayuwa, tsaro da sauran kashe-kashen kudin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262