'Da Haushin Kare Ya Mutu': Rikakken Dan Ta'adda Ya Yi Mutuwar Wulakanci a Zamfara
- Wani fitaccen 'dan bindiga, Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta da ta sa ya fara yin haushin kare
- Rahotanni sun ce ya kamu da wannan cuta mai ban mamaki mako daya da ya gabata, inda ya fara kukan kare kafin ya mutu
- 'Yan kungiyarsa sun tsorata da halin da ya shiga, sun tilasta wa mazauna garin Kizara su yi masa jana'iza a makarantar firamare
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gusau, Zamfara - Hatsabibin dan bindiga mai suna Kachalla Dan Lukuti ya yi wata irin mutuwar wulakanci a jihar Zamfara.
Dan ta'addan wanda aka sani da kai munanan hare-hare a jihohin Zamfara da Katsina, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta ta kukan kare.

Source: Original
Wani dan ta'adda ya yi mutuwar wulakanci
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa Dan Lukuti ya kamu da cutar makonni daya da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cutar ta jawo masa zazzafan hauka, jijjiga mara iyaka, har ma da yin kukan kare tamkar wanda hauka ta kama shi.
Majiyoyin sun bayyana cewa ‘yan kungiyarsa sun kasa kusantarsa saboda tsananin tsoron cutar, hakan ya sa suka nisanta kansu har sai da ya mutu.
Dan Lukuti shugaban 'yan bindiga ne da ke aikata laifuka daga dajin Kokonba a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Ya jagoranci mayaƙa sama da 50 kuma ya kaddamar da hare-hare a Dan Jiloga, Rijiya, Zonai, Magami, da titin Gusau-Magami.
Har ila yau, rikakken dan ta'addan ya fadada ayyukan ta’addanci zuwa karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Yadda aka yi jana'izar marigayin cikin fargaba
Duk da tsoron da ya jefa mutane a lokacin rayuwarsa, kwanakinsa na ƙarshe sun kasance cikin tsananin wahala, inda shaidun gani da ido suka ce ya rika ihu da kukan kare cikin azaba har ya mutu.
'Yan kungiyarsa, saboda tsananin tsoro da imanin aljanu sun kama shi, sun tilasta wa mutanen Kizara su yi masa jana'iza a makarantar firamare ta garin.

Kara karanta wannan
Jami'in Binance da aka tsare ya fadi yadda Abba Kyari ya taimake shi a gidan yari
Ana kyautata zaton cewa cutar da ta kashe shi na iya zama ciwon hauka ko kuma sakamakon azabar zunubansa na ta'addanci.
Gwamna Lawal ya magantu kan sulhu da yan bindiga
A baya, kun ji cewa Gwamnatin jihar Zamfara ta fito ta sake bayani kan matsayarta dangane da yin sulhu da ƴan bindiga a jihar.
Ta bayyana cewa jar yanzu Gwamna Dauda Lawal yana kan matsayarsa ta cewa ba zai hau kan teburin sulhu da ƴan bindiga ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
