Matsalar Tsaro: An Raba Miliyoyi ga Malaman Addini 75 domin Yin Addu'a

Matsalar Tsaro: An Raba Miliyoyi ga Malaman Addini 75 domin Yin Addu'a

  • Karamar hukumar Musawa ta dauki malaman addini 75 domin yin addu’o’i kan matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar Katsina
  • Shugaban karamar hukumar, Dr Habib Abdulkadir, ya bayyana cewa ana biyan malaman kimanin Naira miliyan 4 a kowane wata
  • Dr. Abdulkadir ya ce tun bayan fara shirin, an fara samun zaman lafiya a wasu sassan yankin da ke fama da hare-haren 'yan bindiga

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Karamar hukumar Musawa da ke jihar Katsina ta dauki malaman addini domin yin addu’o’in neman zaman lafiya da kawo karshen ta’addanci a yankin.

Shugaban karamar hukumar, Dr Habib Abdulkadir ne ya bayyana haka yayin wata hira da manema labarai, inda ya ce an zabo malaman daga kungiyoyin addini daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamna zai karya farashin abinci warwas saboda azumin watan Ramadan

Katsina
An dauki malaman addini domin yin addu'a kan tsaro a Katsina. Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa shirin na daga cikin kokarin da ake yi a Katsina domin dakile matsalar tsaro da ta addabi yankuna da dama na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin daukar malaman addini

Shugaban karamar hukumar Musawa, Dr Habib Abdulkadir, ya ce an dauki matakin daukar malaman addini domin yin addu’o’in neman tsaro ne sakamakon matsalar 'yan bindiga.

The Guardian ta rahoto yana cewa duk da ana kokarin yaki da ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da jami’an tsaro, addu’a ita ma hanya ce da za ta taimaka wajen magance matsalar.

Yadda ake biyan malaman kudin addu'a

Dr Abdulkadir ya bayyana cewa ana biyan malaman addini sama da Naira miliyan 4 a kowane wata domin gudanar da wannan aiki na addu’o’i.

Ya ce karamar hukumar ta dauki nauyin ne domin tabbatar da cewa ana yin addu’o’i a kai-a kai domin samun nasarar kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Faɗa ya ɓarke a jami'ar Najeriya, ɗaliba ta yi wa malami kaca kaca a bidiyo

Rahotanni sun kara nuni da cewa an zakulo malaman ne a bangarorin kungiyoyin addini daban daban domin yin addu'o'in.

Tasirin addu’o’in kan matsalar tsaro

Shugaban karamar hukumar ya ce tun bayan fara shirin, an fara samun zaman lafiya a wasu sassan yankin, inda ya bayyana cewa mutane na iya bacci cikin kwanciyar hankali fiye da da.

Haka kuma, ya jinjinawa gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina kan kokarinsu na yaki da ‘yan ta’adda, inda ya ce Musawa za ta ci gaba da ba da hadin kai domin tabbatar da tsaro.

Lamarin na zuwa ne yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da sakin wuta ba dare ba rana a kan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sakin wutar da sojojin ke yi ya sanya dakile 'yan ta'adda da dama tare da tilasta wa wasu da dama mika wuya ga jami'an tsaro kasancewar sun rasa mafaka a daji.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram 129,000 sun tuba, ana ba 800 horo na musamman

An kama mai safarar makami a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun kama wani dan ta'adda yana kokarin wucewa cikin daji da tarin makamai.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya yi amfani da wata mota ne dauke da makamai wanda aka ce zai mika ne ga 'yan ta'adda a jihar Katsina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng