Muhuyi: Hukumar PCACC Ta Dura kan Jami'an Gwamnatin Kano, Ta Cafke Hadimin Abba

Muhuyi: Hukumar PCACC Ta Dura kan Jami'an Gwamnatin Kano, Ta Cafke Hadimin Abba

  • Bincike ya biyo ta kan wasu manyan jami'an gwamnati a jihar Kano waɗanda ake zargi da karkatar da kuɗaɗen jama'a
  • Hukumar yaki da cin hanci da karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a ta jihar Kano (PCACC), ta cafke jami'a uku na ƙaramar hukumar Nasarawa
  • PCACC ta haɗa da hadimin gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, cikin waɗanda ta cafƙe kan zargin karkatar da N105m

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar yaƙi da cin hanci da karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a ta jihar Kano (PCACC), ta cafke hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hukumar PCACC ta cafke hadimin ne mai suna Mustapha Maifada tare da wasu jami'ai uku na ƙaramar hukumar Nasarawa.

Hukumar PCACC ta cafke hadimin Gwamna Abba
Hukumar PCACC ta kama hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Barr. Muhuyi Magaji Rimin-Gado
Source: Facebook

Wane zargi ake yi wa hadimin Gwamna Abba?

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an kama mutanen ne bisa zargin karkatar da kuɗi har Naira miliyan 105.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an da aka kama sun haɗa da daraktan kula da ma’aikata, ma'aji da mai fitar da kuɗaɗe na ƙaramar hukumar.

Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya tabbatar da cafke jami’an a wani saƙon WhatsApp da ya aike da safiyar ranar Talata, 11 ga watan Fabrairun 2025.

"Eh, mun kama su, kuma suna hannunmu."

- Muhuyi Magaji Rimin-Gado

Yadda jami'an suka karkatar da kuɗaɗen

Majiyoyi sun bayyana cewa an umarci jami’an na ƙaramar hukumar da su fitar da N105,000 don wani shiri.

Amma, maimakon su bi wannan umarnin, sai suka ba da takardar cire Naira miliyan 105 ga hadimin gwamnan a watan Nuwamba 2024.

Bayan samun bayanai daga ɓangaren sa ido kan harkokin kuɗi kan badaƙalar, sai hukumar yaƙi da cin hancin ta fara bincike.

PCACC za ta ci gaba da bincike a Kano

"Lokacin da aka yi wa jami’an tambayoyi, sun ce lamarin kuskure ne. Sai dai, la’akari da daɗewar da aka yi tun daga Nuwamba 2024 da kuma wasu shaidu da aka tattara, hukumar ta ƙi amincewa da wannan bayani."

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Kano ta runtuma kora a ma'aikatar shari'a, an samu karin bayani

- Wata majiya

Ƙarin bincike ya nuna cewa hadimin gwamnan ya yi amfani da kuɗin wajen siyan kadarori.

Hukumar PCACC ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Hukumar PCACC ta tsare ciyamomi

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da karɓar ƙorafe-ƙorafen jama'a ta jihar Kano, (PCACC) ta tsare wasu shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi uku.

Hukumar PCACC ta cafke mutanen ne bisa zargin karkatar da kuɗaɗen kwangilar ruwa waɗanda adadinsu ya kai Naira miliyan 660.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng