'Dan Taraba Ya Lashe Gasar Musabaka a Kano, Gwamna Ya Yi Farin Ciki
- Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya taya Hafeez Mujaheed Salihu murnar lashe gasar musabaka ta kasa, wanda kungiyar Izalah ta gudanar a Kano
- Mai taimakawa gwamnan, Hon. Hussaini Isma'il, ya ce nasarar Mujaheed na da nasaba da jajircewarsa a addini , aka ji gwamnan ya yaba da himmarsa
- Gwamna Kefas ya ce wannan nasara ta kara haskaka muhimmancin ilimin addini da tarbiyya, ya sha alwashin inganta bangaren addini da ilimi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jalingo, Taraba - Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya taya Hafeez Mujaheed Salihu murnar lashe kasar musabaka.
Gwamnan ya yi matukar farin ciki bayan Mujaheed ya lashe gasar ta kasa da kungiyar Izalah ta gudanar a jihar Kano.

Asali: Facebook
Gwamna ya yabawa matashi bayan gasar musabaka
Mai taimakawa gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci, Hon. Hussaini Isma'il shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Isma'il ya ce gwamnan ya tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da jajircewa da kuma kokarin Mujaheed a bangaren addinin Musulunci.
A cewar sanarwar da Hon. Isma'il ya sanyawa hannu, Gwamna Kefas ya ce wannan nasara na da alaƙa da muhimmancin ilimin addini da tarbiyya da kuma al'adun jihar Taraba.
Gwamna Kefas ya sha alwashi kan inganta ilimi
Daga bisani, gwamna ya sha alwashin kawo tsare-tsare da za su inganta harkokin ilimi da kuma ɓangaren addini.
Gwamna Kefas bayan nuna farin cikinsa, ya yi masa fatan alheri a rayuwarsa da kuma ci gabansa a bangaren addini.
A ƙarshe, ya bukaci dukkan yan uwa da abokan arziki su taya su murnar wannan nasara da ɗansu ya samu.
“Gwamna Agbu Kefas ya taya Hafeez Mujaheed Salihu murnar lashe gasar musabaka da aka yi a Kano karkashin kungiyar Jama'atul Izalatil Bid'ah wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) bangaren Jos.
"Ya ce tabbas wannan nasara ba ta rasa nasaba da jajircewa da kuma kokarin Mujaheed a bangaren addinin Musulunci.
“Wannan nasara tana da alaka da muhimmancin ilimin addini, tarbiyya da kuma al’adun jihar Taraba.
“Ya yi fatan Allah ya kara masa basira da nasara a rayuwarsa, ya bukaci ‘yan uwa da abokan arziki su taya mu murnar wannan nasara da ɗansu ya samu.”
- Gwamna Agbu Kefas
Musulmai sun sauke wa Gwamna Kefas Alkur'ani
Kun ji cewa musulmi a ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2024 sun gudanar da addu'o'i na musamman ga Gwamna Agbu Kefas a jihar Taraba.
An gudanar da addu'o'in ne a Masallacin Juma'a na Saurara da ke birnin Jalingo domin taimakawa gwamnan samun nasarori a mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng