Gwamna Ya Ɗaga Darajar Addinin Musulunci da Ya Buɗe Babban Masallacin Juma'a
- Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya ƙara faɗaɗa ayyukan da yake yi domin ɗaukaka addinin Musulunci da gyaran tarbiyya
- Gwamna Aliyu ya buɗe masallacin Juma'a na Ruggar Wauru wanda gwamnatinsa ta gyara, ya kuma fara biyan limamai alawus duk wata
- Ahmed Aliyu ya kuma sanar da shirinsa na faɗaɗa ciyarwa a watan Ramadan, ya ce za a ƙara yawan cibiyoyin rabawa mabukata abinci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Gwamnatin Sakkwato ta bayyana shirinta na fadada shirin ciyarwa a watan Ramadan domin taimakawa mabukata da marasa galihu a fadin jihar.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya sanar da hakan a ranar Jumma’a, da yake kaddamar da Masallacin Juma'a na Ruggar Wauru wanda ya gyara a Sakkwato.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai girma gwamnan ya wallafa a shafinsa na manhajar X.
Za a faɗaɗa ciyarwa a watan Ramadan
Ya ce tuni gwamnati ta fara shiri domin azumin Ramadan na 2025, tare da kokarin ƙara yawan abincin da ake rabawa a wuraren ciyarwa.
Gwamna Aliyu ya ce:
"Za mu fadada shirin ciyarwa zuwa wasu yankunan da ba su da wuraren ciyarwa a baya, domin su ma su amfana. Za mu kuma tabbatar da cewa ingancin abincin da ake bayarwa ya fi kyau fiye da yadda aka saba."
Gwamna na ginawa da gyara masallatai
Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na kokari wajen ginawa da gyara masallatai da makarantun Islamiyya a fadin jihar Sakkwato.
Daga cikin masallatan Jumu’a da aka kammala sun hada da, masallacin Sheikh Musa Lukuwa, masallacin Tahsinul Qur’an, masallacin Runjin Sambo, da masallacin Sheikh Gumi.
Sauran masallatan sun haɗa da masallacin Sultan Maccido, masallacin titin sarki Yahaya da masallatai a Yabo da Gwadabawa.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ƙara da cewa ana gyara wasu masallatai a Kebbe, Illela, Shagari, da Kware, domin samar da kyakkyawan wuraren ibada ga al’ummar jihar.

Kara karanta wannan
Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara
Gwamna ya tallafawa Limamai da Ladanai
Gwamnan ya ce don kula da masallatai 90 dake cikin birnin Sakkwato, gwamnati ta ware N300,000 zuwa N500,000 a matsayin kudin gudanarwa a kowane wata.
Haka kuma ya ce an kirkiri sabon alawus ga limamai, na'ibai da ladanai domin ƙarfafa masu gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.
Sabunta Hisbah domin gyaran tarbiyya
Gwamnatin Sokoto ta sake dawo da hukumar Hisbah, wacce ke yaki da munanan dabi’u da kare tarbiyya a jihar.
Gwamnan ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki ba tare da katsalandan daga gwamnati ba, sannan ya bada tabbacin cewa za a ci gaba da tallafa mata domin gudanar da aikinta yadda ya kamata.
A yayin taron, kwamishinan harkokin Addini, Dr. Jabir Sani Mai Hulla, da wakilin Sarkin Musulmi kuma Sarkin Argungu, sun yabawa gwamnan bisa kyawawan shirye-shiryensa na inganta rayuwar al’umma.
Ramadan: Ɗan majalisa ya raba N100m a Sokoto
A wani labarin, kun ji cewa ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato, Abdussamad Dasuki ya rabawa mutanen mazaɓarsa N100m.
Hon. Dasuki ya ba da wannan makudan kuɗaɗe ga kwamitin mutum 35 domin a tabawa talakawan mazaɓarsa gabanin watan azumin Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

