Dabara Ta Fara Karewa Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sojoji Sun Koma Maɓoyar Bello Turji
- Babban hafsan tsaro ya ce Bello Turji da sauran manyan ƴan bindiga sun fara rasa mafaka yayin da sojoji suka ci gaba da kai samame
- Janar Christopher Musa ya ce dakarun soji sun sake hallaka gogaggen ɗan ta'adda kuma sun koma sansanin Bello Turji a Zamfara
- Ya ce wannan hare-hare da sojoji ke kai wa saƙo ne ga ƴan ta'adda su gane cewa ba su da sauran wurin shan ruwa a faɗin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa sojoji sun kara matsawa 'yan ta’adda lamba kuma ba su da mafaka a kasar nan.
Janar Musa ya yi wannan bayani ne a wurin rufe taron kwamandojin rundunonin hadin gwiwa na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Abuja a ranar Juma’a.

Source: Twitter
Babban hafsan tsaron ya ce a yanzu hatsabiban ƴan ta'adda irinsu Bello Turji da Sani Black sun fara rasa mafaka kuma sojoji za su cimma su, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda a Zamfara
Musa ya ce an kashe babban dan ta’adda mai suna Kachana Nafaresh tare da mayakansa da dama a wani samame dakarun tsaro suka kai a dajin Zamfara ranar Alhamis.
Ya kuma ce an kai samame sansanin wani babban dan ta’adda mai suna Sani Black, wanda ya dade yana zama wurin shirya hare-hare a yankin.
"A yayin wannan aiki, sojoji sun shiga sansanin Sani Black tare da kone gidansa, wanda hakan ya sa shi tserewa," in ji Musa.
Janar Musa ya kara da cewa bayan wannan farmaki, dakarun tsaro sun ci gaba da fatattakar 'yan bindiga daga garuruwan Tufan da Mashima, inda suka tilasta musu komawa cikin daji.
Dawowar dakarun tsaro sansanin Bello Turji

Kara karanta wannan
Matsin lamba daga sojoji ya tilastawa Turji da amininsa tserewa, an fadi halin da suke ciki
A wani farmaki mai muhimmanci, Musa ya ce sojoji sun sake komawa sansanin ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, wanda aka taba mutsutsukewa a baya.
"A wannan karon, sojojin sun rusa ragowar sansaninsa, domin tabbatar da cewa babu wani guri da zai sake komawa."
Bayanai sun nuna cewa Bello Turji da Sani Black yanzu haka suna cikin daji suna kokarin gudu daga farmakin sojoji.
Ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Yamma
Shugaban tsaron ya ce ba za a sassauta farmakin da ake kaiwa ‘yan ta’adda a Zamfara da sauran yankunan Arewa maso Yamma ba har sai tsaro ya dawo.
"Wannan farmaki ya nuna cewa gwamnati ba za ta yi sako-sako da lamarin tsaro ba. Wannan sako ne mai karfi ga duk ‘yan ta’adda cewa zamanin aikata laifi ba tare da hukunci ba ya kare."
Ya yi alkawarin cewa za a ci gaba da fatattakar duk wasu kungiyoyin ta’addanci har sai an kawo karshen su gaba daya.
Jami'an tsaro sun ceto mutane a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji da ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindiga, sun ƙwato mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.
Jami'an tsaron sun ceto mutanen da aka sace, a lokacin wani samame na haɗin gwiwa da suka kai a yankin ƙaramar hukumar Kajuru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

