Duniya ba Komai ba: Jarumin Fina Finai Kuma Lakcara Ya Yi Bankwana da Duniya

Duniya ba Komai ba: Jarumin Fina Finai Kuma Lakcara Ya Yi Bankwana da Duniya

  • Fitaccen jarumin Nollywood, Columbus Irisoanga, wanda aka sani da taka rawar boka a fina-finai, ya riga mu gidan gaskiya
  • Shahararriyar jarumar Nollywood Hilda Dokubo shi ya sanar labarin mutuwar marigayin a yau Alhamis 6 ga watan Janairun 2025
  • Dokubo ta bayyana mutuwar Irisoanga a shafinta na Instagram da cewa wannan babban rashi ne ga Nollywood
  • Ban da yin fim, Irisoanga malami ne a Sashen koyon wasan kwaikwayo na Jami’ar Port Harcourt da ke jihar Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Fitaccen jarumin Nollywood, Columbus Irisoanga, wanda aka fi sani da kwarewarsa wajen taka rawar boka a fina-finai, ya rasu..

An tabbatar da rasuwar marigayin ne kuma lakcara a jami'ar Port Harcourt a yau Alhamis 6 g watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano

Jarumin finafinan Nollywood ya riga mu gidan gaskiya
Fitaccen jarumin Nollywood kuma lakcara a jami'ar Port Harcourt ya rasu. Hoto: Hilda Dokubo.
Asali: Facebook

Marashiyar jarumar Nollywood ta rasu

Wata jarumar Nollywood, Hilda Dokubo, ce ta sanar da rasuwarsa a ranar Alhamis ta hannun wani rubutu a shafinta na Instagram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwar Irisoanga na zuwa ne kwana ɗaya bayan sanar da rasuwar matashiya a masana'antar shirya fina-finan Nollywood.

Fitacciyar jarumar a masana'antar Nollywood, Pat Uguwu ta mutu tana da shekara 35 a duniya.

Abokin aikinta a masana'antar, Jarumi Emeka Okoye ne ya sanar da rasuwar matashiyar a shafinsa ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, 2025.

Tuni dai jarumai mata da maza daga Nollywood suka fara tura sakon ta'aziyya da alhinin mutuwar Pat Ugwu tare da yi mata addu'a.

An same rashin fitaccen jarumin fina-finan Nollywood

Jarumi Dokubo a cikin sanarwar ya yada labarin da taken:

“Uncle Coli @colu_mbusirisoanga ya koma ga Ubangiji.
"Wannan babban rashi ne ga jami'ar Uniport da bangaren wasan kwaikwayo da ke jihar Rivers.”

Kara karanta wannan

"Mutuwa mai yankar ƙauna": Matashiyar jarumar fina finai ta riga mu gidan gaskiya

Irisoanga, wanda ya fito daga Jihar Rivers, ba kawai jarumi ba ne, har ila yana koyarwa a sashen koyon wasan kwaikwayo na Jami’ar Port Harcourt.

Ya fito a fina-finai da dama, kuma daga cikin fitattun fina-finan da ya taka rawa akwai "Issakaba" da aka fitar a shekarar 2003.

Maryam Yahaya ta tikiti intanet da sabuwar mota

Kun ji cewa jarumar masana'antar Kannywood, Maryam Yahaya ta samu sabuwar motar Marsandi da ake tsammanin ta kai kimanin Naira miliyan 50.

Sayen mitar fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ya yi wa masoya da masu fatan alheri daɗi bayan labarin ya bazu.

Jarumar ta wallafa hotunan motar a shafukanta na kafafen sada zumunta, inda mutane suka mata rubdugun sakon taya murna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.