Lokaci Ya Yi: Shahararren Malamin Addinin Musulunci a Kaduna Ya Rasu
- An yi rashin ɗaya ɗaga cikin manyan malaman addinin Musulunci a jihar Kaduna, wanda mutane da-dama suke girmamawa
- Sheikh Ishaq Yunus Almadany ya riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairun 2025 bayan ya yi fama da jinya
- Fitaccen malamin addinin musulunci ya yi bankwana da duniya ne dazu a asibitin sojojin sama na 44 da ke cikin birnin Kaduna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Allah ya yi wa shahararren malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Ishaq Yunus Almadany, rasuwa.
Marigayi Sheikh Ishaq Yunus Almadany ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi fama da jinya ta rashin lafiya.

Asali: Facebook
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa malamin addinin musuluncin ya rasu ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ishaq Yunus ya rasu bayan jinya
Marigayin ya bar duniya ne a asibitin sojoji na 44 army reference da ke birnin Kaduna.
Haka kuma masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya tabbatar da rasuwar malamin a shafinsa na Facebook, inda aka yi addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.
Sanarwar na cewa:
"Innaa Lillahi wa Innaa Ilaihi Rajiun, Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus Almadany rasuwa yau a asibitin 44 dake Kaduna."
"Muna roƙon Allah Ya ji ƙansa ya gafarta masa, Ya sa doguwar jinyar da ya yi fama da ita yasa kaffara ce. Allah Ya sa Aljanna ce makomarsa da mu baki ɗaya."
Ƙungiyar Izalah ta yi ta'aziyyar Al Madany
Ƙungiyar Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus Sunnah (JIBWIS) ta tabbatar da rasuwar malamin ta hannun jami'inta na hulɗa da jama'a na kafafen sada zumunta.
Hakazalika shugaban ƙungiyar JIBWIS reshen ihar Kaduna, Alhaji Adamu Ibrahim, ya nuna alhininsa kan rasuwar malamin addinin musuluncin.
Alhaji Adamu Ibrahim ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuran Ya kuma sanya Aljanna ta zama makoma a garesa.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
An gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a filin idi na Sultan Bello, da ke birnin Kaduna.
Sakataren gwamnati a Najeriya ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren gwamnatin jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye, ya yi bankwana da duniya.
Marigayin ya rasu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi, wanda ya sanya ya kwashe lokaci yana jinya a asibiti.
Temitayo Oluwatuyi Oluseye ya zama sakataren gwamnatin jihar Ondo ne a ranar, 24 ga watan Janairun 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng