Tsadar Rayuwa: Wike Ya ba 'Yan Najeriya Mafita kan Manufofin Gwamnatin Tinubu

Tsadar Rayuwa: Wike Ya ba 'Yan Najeriya Mafita kan Manufofin Gwamnatin Tinubu

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya hango alamun nasara a manufofin da gwamnatin Bola Tinubu ta ɓullo da su
  • Wike ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan manufofin shugaban ƙasan duk kuwa da raɗaɗin da suke sha
  • Ministan ya bayyana cewa Tinubu yana da kyakkyawar niyya ga ƙasar nan, kuma za a ga amfanin manufofin da ya kawo nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya jawo hankalin ƴan Najeriya kan mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Nyesom Wike tabbatarwa ƴan Najeriya cewa abubuwa za su yi kyau a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Wike ya ba 'yan Najeriya shawara
Wike ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri da mulkin Tinubu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Ajuri Ngelale
Source: Twitter

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya je ziyarar ta'aziyya ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde kan rasuwar ɗan uwansa, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi wa El Rufai wankin babban bargo, ya fadi wani sirrinsa

Wace shawara Wike ya ba ƴan Najeriya kan Tinubu?

Nyesom Wike ya buƙaci ƴan Najeriya su kai zuciya nesa kan manufofin gwamnatin shugaba Tinubu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

A cewar ministan, Tinubu yana da kyakkyawar niyya ga ƴan Najeriya, domin manufofin da gwamnatinsa ta fito da su, an kawo su ne da nufin gyara ƙasar nan.

"Dangane da halin da ƙasa take ciki a yanzu, abin da zan ce kawai shi ne jama'a su yi haƙuri. Amma wannan ƙasar ta samu sauyi kan yadda take shekaru kaɗan da suka wuce."
"Wannan ƙasar ta shiga mawuyacin hali, kuma idan muna son gyara, dole ne mu yi haƙuri da abin da shugaban ƙasan yake yi. Hakan zai ɗauki lokaci."
"Don haka, dangane da manufofin da shugaba Tinubu ke ƙoƙarin aiwatarwa, mutane za su ji raɗaɗinsu, amma a ƙarshe za mu cimma abin da ya kamata mu cimmawa."
"A wajena babu wanda ya kamata ya tsorata, domin shugaba Tinubu yana da kyakkyawar niyya ga ƙasar, kuma ƴan Najeriya za su ga amfanin hakan."

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi bangaren lafiya, ya yi wa likitoci da sauran ma'aikata gata

- Nyesom Wike

Ministan ya tunatar da cewa ƙasar nan ta kusa rugujewa kafin zuwan wannan gwamnatin kan madafun iko.

A cewarsa, manufofin da gwamnatin Tinubu ta kawo, an samar da su ne bisa buƙatar yin gyara domin abubuwa su inganta a ƙasar nan.

Wike ya samu ƴan rakiya

A yayin ziyarar dai, Nyesom Wike ya samu rakiyar wasu daga cikin mambobin tsohuwar ƙungiyar gwamnoni ta G-5.

Ƴan rakiyar ta sa sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.

Sauran sun haɗa da Sandy Onor, Philip Aduda, Olaka Nwogu, Mao Ohuabunwa, da tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Chibudom Nwuche.

Wike ya fifita Tinubu kan jam'iyyarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shirya goyon bayan tazarcen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Wike wanda mamba ne a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ya nuna cewa ko kaɗan bai yi nadamar yin aiki a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng