'Yan Bindiga: Bola Tinubu Ya Hurowa Shugabannin Tsaron Najeriya Wuta

'Yan Bindiga: Bola Tinubu Ya Hurowa Shugabannin Tsaron Najeriya Wuta

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya ce shugaba Bola Tinubu na matsa lamba domin ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Mohammed Badaru Abubakar ya ce shugaban ƙasa ya tattauna da shugabannin tsaro inda ya nemi jin lokacin da matsalar za ta ƙare
  • Haka zalika Badaru ya tabbatar da cewa shirin kammala magance matsalar tsaro zuwa ƙarshen shekara yana tafiya cikin tsari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na matsa lamba sosai ga hukumomin tsaro.

Mohammed Badaru Abubakar ya bayyana cewa Bola Tinubu na hura musu wuta domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan.

Badaru
Ministan tsaro ya ce an kusa kawo karshen 'yan bindiga. Hoto: Defence Headquarters
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Badaru ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya waiwayi bangaren lafiya, ya yi wa likitoci da sauran ma'aikata gata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin hirar, shugabannin hukumomin tsaro sun yi wata ganawa da shugaban ƙasa domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro cikin gaggawa.

A cewarsa, shugaba Tinubu ya nemi sanin lokacin da matsalar tsaro za ta ƙare, inda shugabannin tsaro suka tabbatar masa cewa za a shawo kan lamarin kafin ƙarshen wannan shekara.

Tinubu ya hura wuta kan matsalar tsaro

Rahoton Pulse Nigeria ya nuna cewa Badaru ya ce shugaba Tinubu na yin tambayoyi a kai-a kai kan matsalar tsaro, yana neman a gaggauta kawo ƙarshen ta.

"Muna ƙarƙashin matsin lamba daga shugaba Tinubu domin kawo ƙarshen matsalar tsaro. A duk lokacin da muka gana da shi, yana tambaya:
"Ya ya batun matsalar tsaro? Wane ci gaba aka samu?’"

- Mohammed Badaru Abubakar

Ya ƙara da cewa shugabannin tsaro sun bayyana wa shugaban ƙasa irin matakan da aka ɗauka, kuma sun tabbatar masa da cewa nan da ƙarshen shekara abubuwa za su daidaita.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano

"Mun yi wata ganawa ta musamman da shugaban ƙasa, manyan hafsoshin tsaro, da mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
"An tattauna abubuwa da dama kuma shugabannin tsaro sun tabbatar wa shugaban ƙasa cewa kafin ƙarshen shekara, lamarin zai daidaita,"

- Mohammed Badaru Abubakar

Badaru ya bayyana cewa shugabannin tsaro sun ɗauki matakai masu tsauri domin shawo kan matsalar tsaro da wuri-wuri.

Ana sa ran cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa an wargaza sansanonin ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuffuka a fadin ƙasar nan.

'Ba a kama Turji ba tukunna' - Badaru

Da yake magana kan shahararren ɗan bindiga, Bello Turji, ministan tsaro ya bayyana cewa har yanzu ba a kama shi ba, amma hukumomin tsaro sun tsananta bincike domin cafke shi.

"Har yanzu ba a kama Bello Turji ba, amma yanzu haka ya firgita. Za mu kama shi nan gaba kaɗan,"

Kara karanta wannan

'Na yi kokari': Buhari ya jero bangarorin da ya kawo sauyi a mulkinsa, an yaba masa

- Mohammed Badaru Abubakar

An kashe 'yan bindiga a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindiga a Alkaleri.

Lamarin ya faru ne bayan wani kazamin fada da 'yan sanda suka yi ne tsakaninsu da 'yan bindiga a wata maboyarsu inda aka kwato makamai da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel