Tsufa Ta Yi Gardama: Jami'an NDLEA Sun Cafke Dan Shekara 75 Mai Safarar Kwayoyi

Tsufa Ta Yi Gardama: Jami'an NDLEA Sun Cafke Dan Shekara 75 Mai Safarar Kwayoyi

  • Dubun wani dattijo mai shekara 75 da ke safarar miyagun ƙwayoyi ta cika a jihar Kano bayan ya shiga hannun jami'an hukumar NDLEA
  • Jami'an na hukumar NDLEA sun yi caraf da dattijon ne a wani samame da suka kai a ƙauyen Tumbau da ke ƙaramar hukumar Gezawa
  • Dattijon mai suna Nuhu Baba ya yi bayanin cewa ya zaɓi ya bi wannan hanyar domin ya riƙa samun abin da zai sanya a bakin salati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar hana sha da tataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta cafke wani tsoho mai shekara 75 mai suna Nuhu Baba.

Jami'an na NDLEA sun cafke dattijon ne yayin wani samame da suka kai a ƙauyen Tumbau da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Jami'an NDLEA sun cafke dattijo a Kano
Jami'an NDLEA sun cafke dattijo mai safarar kwayoyi a Kano Hoto: @official_ndlea
Asali: Twitter

Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi dirar mikiya kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an NDLEA sun cafke dattijo a Kano

Sadiq Maigatari ya bayyana cewa an ƙwato miyagun ƙwayoyi daban-daban a yayin samamen da jami'an hukumar suka kai.

Ya ce ƙwayoyin da suka ƙwato sun haɗa da Tramadol, tabar wiwi, Diazepam, Exol-5, da kuma maganin Rubber Solution.

“A yayin bincike, Nuhu Baba ya amsa cewa ya kwashe tsawon shekara biyu yana gudanar da wannan haramtacciyar sana'a domin samun abin da zai dogara da shi."

- Sadiq Maigatari

Ya jaddada cewa kama dattijon ya nuna irin yadda fataucin ƙwayoyi da amfani da su ke da matuƙar illa, inda matasa da tsofaffi ke faɗawa cikin wannan muguwar ɗabi’a.

Sadiq Maigatari ya nanata cewa hukumar NDLEA ta ƙudiri aniyar yaki da duk wani laifi da ya shafi sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ya kuma buƙaci jama'a su ba da haɗin kai wajen kawo ƙarshen matsalar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Bayan ta karɓi Sanata daga PDP, jam'iyyar APC ta ƙara yin babban kamu a Najeriya

Hukumar NDLEA ta buƙaci a ba ta haɗin kai

Hakazalika, kwamandan hukumar NDLEA na Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya tabbatar da aniyar hukumar wajen ci gaba da yaƙi da fataucin ƙwayoyi a jihar, inda ya yi kira ga jama’a da su ba da goyon baya.

"NDLEA reshen Kano na buƙatar hadin kan jama’a wajen fallasa duk wani aiki da ya shafi fataucin kwayoyi."

- Abubakar Idris-Ahmad.

Ya kuma yi kira ga jama'a da su riƙa sanya ido tare da bayar da rahoto kan duk wani mutum ko wata ƙungiya da ake zargi da hulɗa da haramtattun ƙwayoyi.

NDLEA ta gonar tabar wiwi a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), sun gano wata gona da ake noma tabar wiwi a jihar Kano.

Jami'an na NDLEA a yayin samamen da suka kai, sun cafke wani dattijo wanda ya ke noma gonar tabar wiwin.

Kara karanta wannan

"Zargin baki biyu": Fusatattun mutane sun bankawa gidan basarake wuta a Kano

Dattijon dai yana noma tabar wiwi ne da karas a gonar domin ya yi basaja ta yadda ba za a gano shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng