'Za Mu Dauki Mataki': Abin da Sanusi II Ya Ce da Aka Kashe Mutane wajen Rusau a Kano

'Za Mu Dauki Mataki': Abin da Sanusi II Ya Ce da Aka Kashe Mutane wajen Rusau a Kano

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo bayan dawowa daga Saudiya
  • Mai martaba Sarki Sanusi II ya ce za a kafa kwamitin da zai binciki rikicin fili da ya barke tsakanin garin Zakara da jami'ar BUK
  • An ji cewa rikicin filin wanda ya hada da jami'an tsaro ya yi sanadin rasa rayuka akalla hudu yayin da aka yi yunkurin rusa gidaje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga jama'ar garin Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, da su yi hakuri su zauna lafiya.

Kiran na Sarkin Kano ya biyo bayan tashin hankalin da aka shiga a yankin kan rusa gine-gine da takaddamar filaye tsakanin Zakara da jami'ar Bayero (BUK).

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Sarki Sanusi II ya yi magana da ya ziyarci Rimin Zakara, inda aka kashe mutum 4.
Sarkin Kano Sanusi II ya sanar da matakan warware rigimar fili da ta jawo kashe mutane 4 a Ugogo. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Sarki Kano ya gana da mutanen Rimin Zakara

Mai martaba, Sarki Sanusi II ya yi wannan kiran ne yayin da ya kai ziyara garin bayan dawowarsa daga aikin Umrah a ƙasar Saudiya, inji rahoton Vangaurd.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin jawabi ga al’ummar garin, ya yi kira da su yi hakuri, su bi matakan shari’a, yana mai jaddada cewa tashin hankali ba zai warware matsalar ba.

“Idan rikici ya tashi, mutanenmu ne za su sha wahala. Rikici ba zai warware matsala ba. Muna bukatar mu kare rayuka da dukiyoyinmu,” in ji Sarki.

'Za a kafa kwamitin sasanci' - Sarki Sanusi II

Sarki Sanusi II ya ce za a kafa kwamitin da zai kunshi gwamnati, jami’an tsaro, shugabannin garin Rimin Zakara, da jami’ar BUK domin samar da mafita.

“Muna tattaunawa da gwamna, mahukuntan BUK da jami’an tsaro don tabbatar da adalci. Amma duk wanda ya sayar da filinsa kuma ya karbi kudin to ya hakura.

Kara karanta wannan

An koma ruwa: Hatsabibin dan bindiga da aka sako daga Nijar ya dawo Katsina

“Bai kamata warware wannan matsalar ya ci tura ba. Dole mu zauna tare da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa don nemo mafita mai ɗorewa.”

- Sarkin Kano, Sanusi II.

Majalisar Kano ta yi tir da kisan mutum 4

Tun da fari, mun ruwaito cewa, dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Ungogo, Hon Aminu Sa'adu ya magantu kan rikicin fili a Rimin Zakara.

Hon. Aminu ya shaidawa majalisar cewa jami'an tsaro sun kashe mutane hudu a Zakara a lokacin da aka je rushe gidajen mutane da tsakiyar dare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel