Sarki Ya Jefa Kansa a Matsala, Gwamna Ya Dakatar da Basarake kan Cin Zarafin Dattijo

Sarki Ya Jefa Kansa a Matsala, Gwamna Ya Dakatar da Basarake kan Cin Zarafin Dattijo

  • Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Oba Abdulsemiu Ogunjobi na Orile Ifo na tsawon watanni shida bayan zarginsa da cin zarafin wani dattijo mai shekara 73
  • Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta ya ce dakatarwar ya zama dole saboda rashin da’a da kuma yadda aka ci mutuncin Cif Abraham Areola
  • An yada bidiyon a kafafen sada zumunta ya nuna Oba na la’antar Areola da iyalinsa, yana mai cewa zai hukunta shi saboda tasirinsa a wurin jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abeokuta, Ogun - Gwamnatin Jihar Ogun a ranar Litinin ta dakatar da Olorile na Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi har tsawon watanni shida bisa cin zarafin wani dattijo mai shekaru 73.

Gwamna Dapo Abiodun ya dauki matakin ne bayan basaraken ya ci zarafin dattijon mai suna Cif Abraham Areola.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sarki ya ci mutuncin wani tsoho, ya tilasta shi kwanciya a kan titi

An dakatar da dattijo kan cin mutuncin dattijo
Gwamna Dapo Abiodun ya dakatar da sarki kan cin dattijo mai shekaru 73. Hoto: Samuel Ajayi.
Asali: Facebook

Yadda sarki ya ci mutuncin dattijo a Ogun

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Hon Ganiyu Hamzat, ya sanya wa hannu da aka wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan yada wani bidiyo na tsawon minti biyu a kafafen sada zumunta, inda Oba ya la’anci dattijon da iyalinsa bisa zargin hada baki akansa.

Ya kuma yi barazanar hukunta Chief Areola, yana mai cewa yana da tasiri a wurin jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda.

Halin da Oba ya nuna ya jawo ce-ce-ku-ce mai yawa a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi tir da yadda ya muzanta mutumin.

Gwamnatin Ogun ta dakatar da basarake

Hamzat ya ce an yanke hukuncin dakatar da basaraken ne saboda yadda ya nuna halin rashin da’a ga wani daga cikin al’ummarsa a bainar jama’a.

Kwamishinan ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne tare da hadin gwiwar Majalisar Gargajiya ta Egba, bisa tanadin sashe na 52(1) na dokar Sarakuna da Masarautu ta Jihar Ogun ta 2021.

Kara karanta wannan

Tubabben dan bindiga da ya tuba ya zama malami, ya jagoranci addu'o'i a bidiyo

Sanarwar ta ce:

“Domin kare mutuncin mutane da kuma kiyaye darajar masarautu, Gwamnatin Ogun karkashin Prince Dapo Abiodun ta dakatar da Oba Abdulsemiu Adewale Ogunjobi na Orile-Ifo na tsawon watanni shida.”
“An dauki wannan mataki ne bayan da aka gayyaci basaraken da wanda aka ci zarafinsa zuwa ofishin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta don yin bincike.”
“Wannan hukunci ya zama dole sakamakon kalaman rashin da’a da kuma halin da basaraken ya nuna a bainar jama’a, wanda ya yadu a kafafen sada zumunta.”
“Bayan kammala bincike kan lamarin, an dakatar da basaraken tare da kwace duk wata alama ta masarautar Orile-Ifo har sai an gama binciken sahihancin zarge-zargen da ake masa.”

An kashe rayuka kan rigimar sarauta

A wani labarin, sabon rikici ya barke a garin Esa-Oke da ke Osun bayan nadin Yarima Timileyin Oluyemi Ajayi a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle.

Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki cikin garin, suka bude wuta kan jama’a, lamarin da ya jawo asarar rayuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel