Rikici Ya Barke da Gwamna Ya Nada Sabon Sarki, An Kashe Mutane da Dama
- Sabon rikici ya barke a garin Esa-Oke da ke Osun bayan nadin Yarima Timileyin Oluyemi Ajayi a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle
- Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki cikin garin, suka bude wuta kan jama’a, lamarin da ya jawo asarar rayuka
- ‘Yan sanda sun tabbatar da afkuwar rikicin, yayin da suka ce suna kokarin shawo kan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Mutane da dama sun rasa rayukansu a rikicin da ya barke a garin Esa-Oke, karamar hukumar Obokun da ke jihar Osun, kan nadin sabon sarki.
Rikicin ya biyo bayan nadin Yarima Timileyin Oluyemi Ajayi, injiniyan IT daga Birtaniya, a matsayin Olojudo na Ido Ayegunle.

Asali: Twitter
Mutane sun yi adawa da nada sabon sarki
Mazauna garin sun bukaci gwamnati ta daukaka hakimin yankin a matsayin Olojudo, maimakon nada sabon sarki daga wani gari, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, mutanen garin sun yi korafi cewa wanda aka nada sarkin Ido Ayegunle ba dan Esa-Oke ba ne, shi dan yankin Ilesa don haka ba sa sonsa.
Sarkin gargajiya na Esa-Oke, High Chief Adegboyega Ajiboye, ya ce wasu mutane dauke da bindigogi sun kutsa cikin garin tare da harbe mutane da dama.
An kashe mutane da dama kan nada sarki
Cif Adegboyega ya ce:
"Mutanen sun shigo garin cikin motoci hudu, kowace na dauke da mutum 18, inda suka fara harbi a cikin garin. Ba a san adadin wadanda suka mutu ba."
Rahotanni sun bayyana cewa cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun tafi da hakimin Ido Ayegunle bayan harin da aka kai.
Wani mazaunin Esa-Oke ya ce:
“Gwamna ya nada wani dan Ilesa a matsayin Olojudo, wanda bayan haka ne wasu mutane suka shigo garin suna harbi da bindiga.”
Jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sanda a Osun, Yemisi Opalola, ta ce an dauki matakai don shawo kan rikicin da ya barke.
Nadin sarki ya zama rigima a Osun
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun mamaye fadar Ilesa, jihar Osun, yayin da aka naɗa Clement Adesuyi Haastrup a matsayin basaraken Owa-Obokun na Ijesa.
An rahoto cewa Clement Haastrup ya doke 'yan takara tara a zaben sabon sarkin masarautar da aka gudanar a gundumar Ilesa ta Yamma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng