'Ba Yanzu ba': 'Yan Kasuwa Sun Fadi Lokacin Karya Farashin Fetur a Gidajen Mai
- PETROAN ta ce karya farashin fetur da matatar Dangote ta yi ba zai yi tasiri nan take a gidajen mai ba saboda suna da tsohon mai
- Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa matatar Dangote ta rage farashin fetur zuwa N890 da nufin rage tsadar kayayyaki
- Shugaban PETROAN ya nemi ‘yan kasuwa su rage farashin mai idan suka sayo shi a sabon farashi don tabbatar da adalci ga mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar PETROAN ta bayyana cewa sauke farashin man fetur da matatar Dangote ta yi ba zai fara aiki nan take a gidajen mai ba.
Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya jinjinawa Dangote kan rage farashin, amma ya ce akwai kalubale wajen aiwatar da sauyin cikin gaggawa.

Asali: Getty Images
Matatar Dangote ta sauke farashin mai
Legit Hausa ta rahoto cewa matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N950 zuwa N890, kuma sabon farashin ya fara aiki tun ranar Asabar, 1 ga Fabrairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin Dangote ya ce sauke farashin ya biyo bayan sauyin farashin danyen mai a kasuwar duniya da kuma sauyin kasuwannin makamashi da gas.
A cewar kamfanin, raguwar farashin na nuna adalcin Dangote, kamar yadda a baya aka kara farashi saboda hauhawar kudin danyen mai.
Dangote na fatan karya farashin da ya yi zai sa a samu saukar farashin kayayyaki, rage wahalhalu da kuma kawo sauyi mai kyau a tattalin arziki.
PETROAN ta fadi dalilin jinkirin rage farashin fetur
Shugaban PETROAN ya ce duk da cewa gidajen mai ba za su sauke farashin nan take ba amma ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashi daga lokacin da suka sayo sabon mai.
Ya bayyana cewa yawancin gidajen mai na da man da suka saya a tsohon farashi, hakan zai sa rage farashi ba zai yiwu nan take ba, inji rahoton The Guardian.
Ya ce sauyin farashin ba ya aiki nan take, saboda yawancin 'yan kasuwar sun riga sun sayi mai da tsohon farashi kafin sauyin farashin Dangote.
Duk da haka, kungiyar PETROAN na fatan hadin gwiwa da Dangote da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da adalci a fannin kasuwancin man fetur.
Dangote ya fadi dalilin sauke farashin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an fara jin dalilan da suka sa matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N950 zuwa N890 a ranar Asabar da ta gabata.
Saukar farashin na da alaka da raguwar kudin danyen mai a duniya da kuma kokarin Dangote na cika alkawarinsa kan daidaiton farashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng