Tubabben Dan Bindiga da Ya Tuba Ya Zama Malami, Ya Jagoranci Addu’o’i a Bidiyo

Tubabben Dan Bindiga da Ya Tuba Ya Zama Malami, Ya Jagoranci Addu’o’i a Bidiyo

  • Wani sabon bidiyo ya nuna tubabben dan bindiga, Kachallah Bugaje yana jagorantar addu’a tare da yaransa, bayan da ya ce ya daina ta’addanci
  • Bugaje ya bayyana cewa ya saki fiye da mutum 50 da ya yi garkuwa da su ba tare da karɓar kudin fansa ba saboda tsoron Allah
  • Wasu na ganin nadamarsa gaskiya ce, yayin da wasu ke zargin yana kokarin tserewa hukunci ne daga jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Wani sabon bidiyo ya bayyana yana nuna Kachallah Bugaje, shahararren jagoran ‘yan bindiga yana jagorantar addu’a tare da yaransa.

Buhaje wanda ya sauya suna zuwa Zakiru Bugaje yana daga cikin hatsabiban yan bindiga da suka addabi Arewa maso Yammacin Najeriya.

Tubabben dan ta'adda ya jagoranci addu'o'i bayan ajiye makami
Zakiru Bugaje da ya duba daga ta'addanci ya jagoranci addu'o'i da yaransa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Kachallah Bugaje ya tuba daga ta'addanci

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Wannan faifan bidiyo na tsawon minti biyar, wanda Zagazola Makama ya samu, ya jawo cece-kuce kan yadda Bugaje ke jagorantar addu'o'in.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan ya ce shi da mutane 50 daga cikin yaransa sun daina aikata miyagun laifuka kamar garkuwa da mutane da karɓar kudin fansa.

A wani tsohon bidiyo, Bugaje ya amsa cewa ya sace fiye da mutum 50, yana neman kudin fansa daga naira miliyan 10 zuwa miliyan 25.

Sai dai ya ce daga bisani sun saki mutanen ba tare da karɓar ko kwabo ba, yana mai cewa tsoron Allah ne ya sa su yin hakan.

Bugaje ya bayyana nadama sosai kan abubuwan da suka aikata, inda ya roki sauran ‘yan bindiga da su ajiye makamansu.

Ya kuma jinjinawa Annabi Muhammadu (SAW), yana mai kira ga tsoffin abokan aikinsa da su rungumi hanyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Bauchi: Ana zargin kwamishina da sace yarinya, wanda ake tuhuma ya fayyace lamarin

Bugaje ya jagoranci addu'o'i a wani bidiyo

Bugaje, wanda a baya-bayan nan ya bayyana cewa ya bar ta’addanci kuma ya sauya suna zuwa Zakiru Bugaje, an gan shi a bidiyon yana addu’a da mabiyansa.

Duk da haka, fitowar wannan bidiyo ya haifar da shakku a tsakanin mutane, inda wasu ke cewa hakan wata dabara ce don gujewa hukunci.

Wasu naganin Bugaje ya yi hakan ne domin kawai ya dauki hankulan jama'a wurin yin amfani da bidiyon da aka nuna yana jagorantar adduo'i na 'Salatul Fati'.

Wasu kuwa na ganin wannan ikirari na iya zama wata nasara a yunkurin da ake na kawo karshen rashin tsaro a yankin.

Yan bindiga sun yi ta'asa a Plateau

Kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kashe mutum biyar a kauyen Lighitlubang da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikakken dan bindiga ya tuba daga barna bayan sakin wadanda ya kama, ya sauya suna

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun kai farmaki ne da dare lokacin da mutanen kauyen ke barci, inda suka yi yankan rago ga wasu mutane da dama yayin harin.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da aika jami'an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin da abin ya faru domin daukar matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.