An Shiga Jimami bayan Mutane 30 Sun Kone Kurmus a Mummunan Hatsarin Mota
- Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da fasinjoji a jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
- Hatsarin motan wanda ya ritsa da wasu motocin haya guda biyu, ya jawo asarar rayukan aƙalla mutane har guda 30
- Kwamandan hukumar kiyayye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo, ya ve hatsarin ya auku ne bayan motocin guda biyu sun yi karo da juna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Aƙalla fasinjoji 30 ne suka ƙone ƙurmus a mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Ondo.
Mummunan hatsarin motan ya auku ne a yankin Onipetesi da ke kan titin Ore-Lagos, a ƙaramar hukumar Odigbo ta Jihar Ondo.

Asali: Original
Mutane sun ƙone a hatsarin mota
Jaridar Tribune ta ce wani ganau ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da mutane 32, inda mutum 28 suka ƙone ta yadda ba za a iya gane su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mutum biyu da aka ceto da raunuka masu muni suka rasu kafin a kai su asibiti, yayin da mutum biyu kuma har yanzu suna karɓar magani.
Ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da manyan motocin haya guda biyu da suka yi karo da juna, sannan suka kama da wuta nan take, inda fasinjojin suka ƙone ba tare da an iya gane su ba.
Ya danganta hatsarin da gudu fiye da ƙima da direbobin motocin suka yi.
Me hukumomi suka ce kan hatsarin?
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ondo, Dakta Samuel Ibitoye, ya ce mutum 30 sun rasa ransu a hatsarin.
A cewar Ibitoye, jimillar mutane 28 sun ƙone ƙurmus ta yadda ba za a iya gane su ba, yayin da mutum biyu suka rasu a hanyarsu ta zuwa asibiti, sai kuma mutum biyu da ake jinya a asibiti.
Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne lokacin da motocin na haya guda biyu suka yi karo da juna, sannan suka kama da wuta.
Kwamandan na FRSC ya ce binciken farko ya nuna cewa ɗaya daga cikin direban motocin ya sauka daga hannunsa, lamarin da ya haddasa hatsarin a ranar Asabar.
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin, sannan an kai waɗanda suka jikkata asibiti, yayin da aka ajiye gawarwakin mamatan a ɗakin ajiyar gawa na asibiti.
Ibitoye ya yi kira ga direbobi da su riƙa taka tsantsan, su tabbatar da kula da lafiyar motocinsu, kuma su guji tukin ganganci.
Haka kuma, ya bukaci fasinjoji da su dinga yin magana idan suka ga direbobi suna tukin ganganci, yana mai jaddada cewa kiyaye hatsari a kan hanya nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.
Direban mota ya auka kan sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani direban mota ya auka kan sojoji bayan sun fito motsa jiki a jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yamma.
Direban wanda ake zargin yana cikin maye ne, ya auka kan jami'an tsaron ne wanda hakan jawo aka samu asarar rayukan da yawa daga cikinsu.
Asali: Legit.ng