'Ana Yunkurin Farmakar Musulmai a Kudancin Najeriya,' Kungiyar MURIC Ta Tona Asiri

'Ana Yunkurin Farmakar Musulmai a Kudancin Najeriya,' Kungiyar MURIC Ta Tona Asiri

  • Kungiyar MURIC ta zargi wasu kungiyoyi da shirin haddasa rikici kan batun kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma
  • A cewar MURIC, ana amfani da kafofin sada zumunta wajen tunzura jama’a da kuma yin barazana ga shugabannin Musulmi
  • Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tsawatarwa mutanensa da ke barazanar farmakar Musulamn da ke a Kudu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta zargi wasu kungiyoyi da shirin haddasa tashin hankali ga Musulmin Kudu maso Yamma.

Kungiyar ta bukaci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Darakta Janar na DSS da sauran jami’an tsaro su dakile yunkurin kuma su kare rayukan Musulmi.

MURIC ta yi magana kan barazanar da ake yiwa Musulmi a yankin Kudu maso Yamma
MURIC ta yi gargadi kan barazanar farmakar Musulmi a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci. Hoto: @IshaqAkintola
Asali: Twitter

MURIC na zargin ana shirin farmakar Musulmai

MURIC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Juma’a kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarki ya aikawa sarkin Musulmi wasika, an fada masa illar kafa shari'ar Musulunci a Kudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Ishaq ya ce ana yin barazanar da ake yadawa a bidiyo da rubuce-rubuce a soshiyal midiya da nufin farmakar Musulmin Yarbawa da ke goyon bayan kafa shari'ar Musulunci.

Ya ce kungiyoyi daban-daban na Yarbawa su ke yin wadannan barazanan, ciki har da Ahmed Saliu Olokoju, sakataren kungiyar Yarbawa ta YOISF.

Abin da sanarwar MURIC ta kunsa

Sanarwar ta ce:

"A cikin wata makala mai taken ‘Shari’a a Yankin Yarbawa: Shirin Fulani na Halaka Yarbawa,’ Olokoju ya kira Musulmin Yarbawa da suka goyi bayan Shari’a da ‘wakilan Fulani.’ Wannan nuna kabilanci ne da tunzura wata kabila kan wata."
"Haka kuma, ya ambaci sunayen shugabannin Musulmi da wani fitaccen basarake Musulmi a yankin.
"Ya kuma yi barazanar kai hari ga masu goyon bayan kafa shari'ar Musulunci, inda ya ce za su farmake su, iyalansu da kasuwancinsu.
"Olokoju ya bukaci jama’a su shiga kungiyarsa don samun horo na ayyukan ta’addanci da nufin kai hari ga Musulmin Yarbawa."

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi?: Atiku ya ki halartar taron manyan kusoshin PDP da aka yi a Bauchi

MURIC ta aika sako ga fadar shugaban kasa

MURIC ta bukaci jami’an tsaro su dauki wannan barazana da muhimmanci su kuma gaggauta daukar mataki don karewa Musulmin yankin Yarbawa.

"Bai kamata fadar shugaban kasa ta yi biris da wadannan barazana da ke fitowa daga mutanen shugaban kasar ba. Lallai Aso Rock ta mayar da hankali kan abin da ke faruwa."

- Farfesa Ishaq.

Kungiyar ta ce dukkan barazanar da aka samu daga Kudu maso Yamma na zuwa ne daga kungiyoyin Yarbawa da ke adawa da Musulmin yankin.

Ta bukaci Musulmi su ci gaba da zama masu hakuri da bin koyarwar zaman lafiya kamar yadda Majalisar Musulmi ta Najeriya (NSCIA) ta tanada.

Shari'a a Kudu: An aika sako ga Sarkin Musulmi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Oba OmoTooyosi Adebayo M. Akinleye, ya aikawa sarkin Musulmi wasika kan takaddamar kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.

Sarki a yankin Yarbawa ya nuna goyon bayansa ga masu adawa da shari'ar Musulunci a yankin, yana mai cewa hakan na iya kawo barazana ga zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel