Kaduna: Musulunci Ya Samu Karuwa da Kirista Ta Karbi Kalmar Shahada, an Shawarce ta

Kaduna: Musulunci Ya Samu Karuwa da Kirista Ta Karbi Kalmar Shahada, an Shawarce ta

  • Wata mata mai suna Fatima ta Musulunta a Kaduna, inda Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya ba ta kalmar shahada yayin karatunsa a masallaci
  • Malamin ya ja hankalinta kan bin tafarkin Musulunci da aikata ibada bisa Sunnah, tare da yin hakuri idan ta hadu da marasa kyawawan halaye
  • Ya yi mata addu'a Allah ya tabbatar da ita kan tafarkin addini, tare da yi mata fatan alheri a sabon matakin rayuwarta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Addinin Musulunci ya samu karuwa bayan Musuluntar wata baiwar Allah a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Matar wacce ta bayyana sunanta da Fatima ta karbi kalmar shahada a hannun Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah.

Assadussunnah ya ba wata mata kalmar shahada a Kaduna
Wata mata ta musulunta a Kaduna inda Sheikh Yusuf Assadussunnah ya ba ta kalmar shahada. Hoto: Abdullahin Gwandu TV.
Asali: Facebook

Wata mata Kirista ta Musulunta a Kaduna

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnan Filato ya yi magana kan rade radin hana kiran sallah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Assadussunnah ya ba ta kalmar shahada yayin wani karatu da yake gudanarwa domin fadakar da al'umma.

Shehin malamin ya ba ya shawara kan dogewa kan tafarkin Muslunci tare da yin ibada bisa Sunnah.

Sheikh Assadussunnah ya shawarci wacce ta Musulunta

"Abin da kika gani na kyawawan dabi'u na Musulunci ko kin hadu da wani wanda ya miki ba daidai ba, ki dauka cewa abin da ya yi ya sabawa Musulunci saboda addinin daban shi daban.
"Abin da ke faruwa, Musulmi ne kaɗai ake hukunta su da abin da wani ya yi amma duk ragowar al'umma ba a musu haka.
"Misali idan wani ya dasa bam a wani wuri saboda shi Musulmi ne sai a hukunta Musulunci a ce shi ya koyar da wannan, shi daban, Musulunci daban."

- Sheikh Assadussunnah

Sheikh Assadussunnah ya yi mata addu'ar Allah ya tabbatar da ita tafarkin addini inda ya yi mata fatan alheri a cikin sabon rayuwa da ta shiga.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya ba tsohon dan majalisa mukami, ya ba wasu 2 kujeru a gwamnati

Wani ya fuskanci matsala bayan Musulunta

A wani labarin, wani magidanci mai suna Yahaya ya kai ƙarar matarsa gaban kotu a birnin Tarayya Abuja, ya nemi a raba aurensu saboda banbancin addini.

Magidancin ya shaidawa alkali cewa ya auri matar ne lokacin yana Kirista, daga bisani kuma ya musulunta, tun daga nan zaman lafiya ya bar gidansa.

Ya roki kotun ta raba auren sannan ta ba shi damar riƙe ɗaya daga cikin ƴaƴa biyu da suka haifa a zaman aurensu da haka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel