Sauƙi Ya Samu: Dangote Ya Ƙara Sauke Farashin Man Fetur, Ya Faɗi Sabon Farashi
- Matatar Dangote ta rage farashin litar mai daga N950 zuwa N890, tana mai cewa ragin ya biyo bayan raguwar farashin danyen mai
- Kamfanin Dangote ya bukaci masu sayar da mai da su tabbatar da cewa raguwar farashin ta kai ga talakawa don rage tsadar rayuwa
- Jama’a na jiran ganin ko gidajen man ‘yan kasuwa za su saukar da farashim yayin da Legit Hausa ta ji bakin wasu kan matakin Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur da take sayarwa a matatar, wanda zai fara aiki ranar Asabar, 1 ga Fabrairu, 2025.
A kokarin rage wa ‘yan Najeriya radadin hauhawar farashi, Dangote ya saukar da farashin mai daga N950 zuwa N890 kan kowace lita.

Asali: Getty Images
Dangote ya sauke farashin fetur
Kamfanin Dangote ya sanar da hakan a shafinsa na X a yammacin Asabar, yana mai cewa raguwar ta biyo bayan saukar farashin danyen mai a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da Anthony Chiejina, Jami’in Dangote Group mai kula da sadarwa, ya sanyawa hannu, ta ce rage farashin na da alaka da yanayin kasuwannin makamashi.
"Sauke farashin yana da nasaba da sauyin yanayin kasuwar makamashi ta duniya da kuma raguwar farashin danyen mai a kasuwannin kasa da kasa."
- Anthony Chiejina.
Litar fetur ta koma N890 a matatar Dangote
Tunda farashin mai yana tasiri kan sufuri da kayayyaki, wannan saukar farashin zai taimaka wa 'yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa.
"Matatar Dangote na da yakinin cewa rage farashin daga N950 zuwa N890 zai taimaka wajen rage tsadar kayayyaki da rayuwa," a cewar kamfanin.
Dangote ya bukaci ‘yan kasuwar mai su tabbatar da cewa rage farashin man ya amfanar da talakawa ta hanyar saukar da farashin da suke sayarwa a gidajen mansu.
Dangote zai taimakawa kudurin Tinubu
Kamfanin ya kuma bayyana kudurinsa na tallafa wa shirin farfado da tattalin arziki na gwamnatin Bola Tinubu da nufin kawo wadatuwa da isasshen mai a Najeriya.
Yayin da jama’a ke maraba da wannan ragin farashin, hankula sun karkata kan ko gidajen mai da ‘yan kasuwa don ganin ko za su bi sahun Dangote wajen rage farashin.
Masu ababen hawa da ‘yan kasuwa na jiran ganin sauyin da rage farashin zai kawo, tare da fatan za a tabbatar da saukar farashin a duk fadin kasar.
An yabawa kokarin matatar Dangote
A zantawar Legit Hausa da wani tsohon dan kasuwar mai, Alhaji Babangida Katsina, ya ce abin da matatar Dangote ke yi abin a yaba ne.
Alhaji Babangida ya ce:
"Duk da cewa har yanzu ana sayen man da tsada, amma dole mu yabawa Dangote saboda yana gaggauta sauke farashi ko karawa gwargwadon farashin man a kasuwar duniya.
"Sai dai ba a nan ne gizo yake tasa sakar ba, domin Dangote kadai ba shi zai sa farashin mai ya sauka a gaba daya Najeriya ba, dole sai da hadin kan 'yan kasuwa."
Alhaji Babangida ya ce matsalar da aka dade ana fuskanta a Najeriya ita ce wasu 'yan kauwa ba sa son rage farashin kaya idan ya ragu a duniya, saboda son zuciya.
"Ya kamata ace, cikin 'yan kwanaki kalilan a ga wannan canjin a gidajen man da ke fadin kasar nan, saboda sun sayo shi da araha. To amma ka san 'yan kasuwar mu, suna gaggawar karawa kaya farashi, amma suna jinkirin sauke farashin."
- Alhaji Babangida.
"Farashin fetur zai karye a Najeriya" - PETROAN
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar 'yan kasuwar mai ta PETROAN ta ce farashin fetur zai ragu bayan farfaɗo da matatun man Fatakwal da Warri.
PETROAN ta bayyana cewa matatun sun fara aiki sosai, kuma a halin yanzu, 'yan ƙungiyar na ci gaba da karɓar fetur daga wurin.
Asali: Legit.ng