Gwamna Zulum Ya Tuna da Iyalan Babban Jami'in Sojan da 'Yan Boko Haram Suka Kashe
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya tuna da iyalan marigayi Laftanal Kanal Thomas Alari wanda ya rasu a fagen daga
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba iyalan marigayin gudunmawar kuɗi N30m tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa a gare su
- Gwamnan ya kuma ba iyalan marigayin wanda ya rasa ransa a yaƙi da ƴan Boko Haram cewa zai ci gaba da tallafa musu da na sauran sojojin da suka rasu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da gudunmuwar N30m ga iyalan marigayi Laftanar Kanal Thomas Alari.
Gwamna Zulum ya ba da gudunmawar kuɗin ne bayan marigayin ya rasa ransa a ci gaba da yaƙin da ake yi da Boko Haram a yankin Timbuktu Triangle.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya miƙa gudunmuwar kuɗin ne da kansa ga matar marigayin a ranar Asabar a birnin Maiduguri.

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Zulum ya ba da gudunmawa
Gwamna Zulum ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da duk waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin da ake yi da ƴan ta'adda a Borno da yankin Arewa maso Gabas baki ɗaya.
"Jiya, mun aika manyan jami’an gwamnatin jiha zuwa wajen jana'izar."
"Duk da haka, na ga dacewar na zo da kaina domin in miƙa ta’aziyyata a madadin gwamnati da al’ummar jihar."
- Gwamna Babagana Zulum
Gwamnan ya ba iyalan marigayin tabbaci
Ya bayyana cewa gudunmuwar da aka bayar na da nufin taimakawa iyalan marigayin wajen sayen gida, duba da cewa bai mallaki gidan kansa ba kafin rasuwarsa.
"Muna ba da gudunmuwar N30m ga iyalansa domin su sayi gida saboda an shaida min cewa Laftanar Kanal Alari bai mallaki gidan kansa ba."
"Ina so in tabbatar muku cewa, banda wannan, za mu ci gaba da tallafa muku da kuma iyalan gwarazan sojojinmu da suka sadaukar da rayukansu domin kare ƙasarmu."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
An miƙa gudunmuwar ne a gaban kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Waidi Shuaibu, kwamandan sashen na biyu, Manjo Janar Chieiebere Ejike, da wasu manyan jami’an gwamnati.
Gwamna Zulum ya gargaɗi jama'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ja kunnen mutanen da ke zaune a ƙauyukan ƙaramar hukumar Baga ta jihar.
Gwamnan ya yi gargaɗi mutanen kan cewa ka da su riƙa haɗa kai da ƴan ta'addan Boko Haram domin yin hakan babbar barazana ce ga tsaro.
Asali: Legit.ng