Gwamnan Sokoto Ya Mika Bukatarsa ga Shugabannin Tsaro kan 'Yan Bindiga

Gwamnan Sokoto Ya Mika Bukatarsa ga Shugabannin Tsaro kan 'Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi magana kan nasarorin da aka samu game da matsalar rashin tsaro
  • Ahmed Aliyu ya buƙaci sababbin shugabannin hukumomin tsaron da aka tura zuwa jihar da su kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga
  • Gwamnan ya yi jira a gareɓsunda su nuna jajircewa da ƙwazo irin na waɗanda suka gabace su domin sauke nauyin da aka ɗora musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi kira ga sababbin shugabannin hukumomin tsaro da aka tura zuwa jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya buƙaci sababbin shugabannin hukumomin tsaron da su ƙara ƙaimi a yaƙi da ƴan bindiga a jihar.

Gwamnan Sokoto ya yi ga shugabannin tsaro
Gwamnan Sokoto ya bukaci shugabannin tsaro su kawo karshen 'yan bindiga Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin da shugabannin tsaron suka kai masa ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Sokoto, babbar birnin jihar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya kasa hakura, ya yi wa ministan Tinubu martani mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Sokoto ya yi kira ga shugabannin tsaro

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen yaƙi da rashin tsaro, don haka yana fatan sababbin shugabannin tsaron za su ci gaba da ginawa kan waɗannan nasarorin.

“Muna samun gagarumar nasara a yaƙin da muke yi da ƴan bindiga a jihar, don haka muna sa ran za ku bada gudunmawa mai kyau a wannan fannin."

- Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamnan ya buƙaci shugabannin tsaron da su yi koyi da waɗanda suka gabace su ta fuskar jajircewa, ƙwazo da sadaukarwa, yana mai jaddada buƙatar yin aiki tare domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana mutanen Sokoto a matsayin masu zaman lafiya da bin doka.

Ya kuma buƙaci shugabannin tsaron su yi aiki tare da al’ummar jihar domin samar da yarda da haɗin kai a tsakaninsu.

“Mutanenmu masu karamci ne, kuma suna maraba da duk wanda ya zo domin aiki ko zama tare da su."

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

- Gwamna Ahmed Aliyu

Gwamna Aliyu zai ba jami'an tsaro goyon baya

Aliyu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ba su cikakken goyon baya wajen samar da dukkan kayayyakin da suke buƙata domin sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata.

Duk da matsalolin ƴan bindiga da suka addabi jihar sama da shekaru goma, gwamnan ya yabawa juriyar al’ummar jihar tare da godewa hukumomin tsaro kan ƙoƙarin da suke yi domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnatin Sokoto ta ankarar da jama'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta ankarar da mutanen gabashin jihar kan barazanar ƴan ta'adda.

Gwamnatin ta buƙaci ta mutanen yankin da su yi taka tsan-tsan da ƴan ta'addan da suke guduwa daga cikin dazuzzuka sakamakon ruwan wutan da sojoji suke yi musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel