Shugaban EFCC Ya Fadi Halin 'Yan Najeriya Mai Kawo Cikas ga Yaki da Cin Hanci
- Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede ya nuna damuwa kan halayyar ƴan Najeriya dangane da cin hanci
- Ola Olukoyede ya koka kan cewa ƴan Najeriya na sukar cin hanci amma suna goyon bayan shugabannin da aka samu da laifin rashawa
- Shugaban na hukumar EFCC ya bayyana cewa yaƙi da cin hanci da rashawa yana buƙatar samun haɗin kai daga wajen al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya koka kan halin ƴan Najeriya dangane da cin hanci da rashawa.
Shugaban na hukumar EFCC ya ce ƴan Najeriya na la’antar rashawa amma sukan goyi bayan shugabanni masu cin hanci idan aka gurfanar da su a kotu.

Asali: Facebook
Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja lokacin da jami’an cibiyar CCC, ƙarƙashin jagorancin Chris Olukolade, daraktan kwamitin amintattunta, suka kai masa ziyara, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban EFCC ya ba ƴan Najeriya shawara
Shugaban na EFCC ya ce rashin ci gaban da ake fama da shi zai zama tarihi idan kowane ɗan ƙasa ya ɗauki cin hanci da rashawa a matsayin abokin gaba.
"Ɗaya daga cikin manyan matsalolin Najeriya, wanda idan aka magance shi, zai kawo ƙarshen rashin ci gaba, shi ne cin hanci da rashawa."
“Al’umma da ke son ci gaba, alhakin hakan ba wai kawai yana kan gwamnati ba ne, har da al’ummar kanta."
“Wannan shi ne dalilin da ya sa muka jajirce sosai a kan wannan aiki. Mun shirya tsaf domin aiwatar da abin da ya kamata mu yi, a bisa tanadin doka da ikon da kundin tsarin mulki ya ba mu."
"Idan kowa ya yanke shawarar yin abin da ya dace, Najeriya za ta ci gaba."
- Ola Olukoyede
Shugaban na EFCC ya ce haɗin gwiwa da CCC zai ƙarfafa dabarun sadarwa da hulɗa da jama’a, yana mai jaddada cewa goyon bayan al’umma yana da matuƙar muhimmanci ga nasarar EFCC.
Ya ce EFCC za ta haɗa kai da CCC domin wayar da kan jama’a game da ayyukanta da kuma mahimmancin riƙon amana a tsakanin ƴan Najeriya.
Shugaban EFCC ya koka kan halin ƴan Najeriya
“Abin takaici ne cewa mutanen da ke sukar rashawa su ne kuma suke kare masu cin hanci."
“Kowa na ƙorafi cewa ƴan Najeriya na da cin hanci, cewa cin hanci yana kashe mu kuma yana lalata tsarinmu, amma idan muka binciki manyan mutane kuma muka gurfanar da su a kotu, su ne kuma za su fito da alluna suna goyon bayansu."
“Wannan ba ya nuna cewa mun ɗauki yaƙin da gaske. Wannan yaƙin yana buƙatar hadin gwiwa."
- Ola Olukoyede
EFCC ta tsare jami'anta
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa dukiyar ƙasa ta'annati (EFCC), ta tsare wasu daga cikin jami'anta.
Hukumar yaƙi da cin hancin ta tsare jami'an nata ne guda 10 bisa zargin satar kayan aiki a ofishinta da ke birnin Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng