Rikakken Dan Bindiga Ya Tuba daga Barna bayan Sakin Wadanda Ya Kama, Ya Sauya Suna

Rikakken Dan Bindiga Ya Tuba daga Barna bayan Sakin Wadanda Ya Kama, Ya Sauya Suna

  • Rikakken ɗan bindiga, Kachallah Bugaje ya tuba daga ta’addanci tare da mayaƙansa 50, inda ya saki mutane 50 da ya yi garkuwa da su
  • A cikin wani faifan bidiyo, Bugaje ya ce daga yanzu a kira shi Zakiru Bugaje, ya kuma bayyana cewa ya daina satar mutane da sata gaba ɗaya
  • Dan ta'addan ya ce sun karɓi fansa har miliyan 25 amma daga baya suka saki mutanen ba tare da cin kuɗi ba, saboda tsoron Allah SWT
  • Wannan na zuwa ne yayin da rundunar sojoji ke kafa kaimi domin kakkabe yan ta'adda da suka addabi yankin Arewa maso Yamma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wani daga cikin fitattun yan bindiga ya ba mutane mamaki bayan tuba daga ta'addanci da kuma sauya sunansa da ake kira.

Shugaban ’yan bindiga, da aka fi sani da Kachallah Bugaje, ya bayyana cewa ya tuba daga ta’addanci tare da mayaƙansa 50, kuma ya daina aikata miyagun laifuffuka.

Kara karanta wannan

'Na rasa budurcina': Bobrisky ya fadi yadda ya dirka wa budurwa ciki a jami'a

Shugaban yan bindiga ya tuba daga ayyukan ta'addanci
Rikakken dan ta'adda, Kachallah Bugaje ya waysar da ayyukan ta'addanci. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Shugaban yan bindiga ya tuba daga ta'addanci

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Zagazola Makama ya wallafa a X a daren yau Juma'a 31 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna 5 da daƙiƙa 42, Bugaje ya ce yanzu yana son a kira shi Zakiru Bugaje, ya ce ya daina satar mutane da sata gaba ɗaya.

“Muna sace mutane sama da 50, muna kiran iyalansu, muna neman fansa, wasu har miliyan 10, wasu miliyan 25.
"Amma daga baya mun sake su ba tare da karɓar ko sisin kwabo ba, saboda tsoron Allah."

- Kachallah Bugaje

Bugaje ya ba yan ta'adda shawara

Bugaje ya jaddada nadamarsa kan abubuwan da ya aikata a baya, yana mai tabbatar da cewa ba zai sake komawa harkar ta’addanci ba.

Dan bindigan ya yi yabo ga Annabi Muhammadu (SAW), yana kuma kira ga sauran ’yan bindiga da su bar wannan mummunar hanya, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga uku a Najeriya, dakarun sojoji sun hallaka sama da 350

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji

Kun ji cewa Rundunar Sojojin Najeriya, a karkashin Operation Hadarin Daji, ta kara kaimi a kokarin da ta ke na shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji.

Wannan bayanin ya na zuwa ne a lokacin da ake rade-radin cewa an cafke jagoran 'yan ta'addan, lamarin da rundunar ta musanta.

Dakarun sun bayyana cewa ba za ta huta a yaki da ta'addanci ba, har sai an kama kasurgumin dan ta'addan da ya addabi jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel