Lauyoyi da Ma'aikata Sun Hango Mutuwa Ana cikin Shari'a, Sun Yi Rige Rigen Ficewa daga Kotu

Lauyoyi da Ma'aikata Sun Hango Mutuwa Ana cikin Shari'a, Sun Yi Rige Rigen Ficewa daga Kotu

  • Alkalai, lauyoyi da ma'aikata sun gaggauta fita daga harabar babbar kotun jihar Imo da ke Owerri a lokacin da ginin mai hawa uku ya motsa
  • Bayanai sun nuna cewa an yi ginin kotun ne a zamanin mulkin tsohon gwamnan Imo, Sanata Rochas Okoroch kuma da alama ba a yi mai ƙwari ba
  • Lauyoyi da sauran masu amfana da kotun sun yi kira ga hukumomi su ɗauki matakin duba lafiyar ginin domin kare rayukan masu aiki a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Lauyoyi sama da 20 sun dakatar da zaman shari'a a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri a Kudu maso Gabashin Nsjeriya.

Lauyoyi da sauran ma'aikata sun yi rige-rigen ficewa daga harabar kotun domim tsira da rayuwarsu yayin da suka fahimci ginin kotun mai hawa uku ya fara girgiɗi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fara taɓa manya, an yi garkuwa da shugaban hukumar zaɓe ta jiha

Taswirar jihar Imo.
Ginin kotu ya motsa ana tsaka da zaman shari'a a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahotan jaridar The Naton ya bayyana cewa an gina wannan ginin kotu ne a zamanin tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ginin kotu ya tilastawa lauyoyi guduwa

Amma dai ana zargin ginin ba shi da inganci da tsari mai kyau saboda yana motsi sosai idan mutane suka masa yawa.

Wannan damuwa ta sa lauyoyi da ma’aikatan kotu ficewa daga harabar kotun domin kauce wa hatsari bayan sun fahimci ginin ya fara girgizawa.

Shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Owerri, Barrister Chris Ihentuge, ya bayyana damuwa kan girgizar da ginin kotu ke yi yayin zaman shari’a.

Da yake jawabi ga abokan aikinsa da masu shari’a a harabar kotu a ranar Juma’a, Ihentuge ya ce an sha samun girgizar ginin yayin da ake shari’a a cikin kotun.

Ginin kotun mai hawa 3 ya jima yana girgiza

A rahoton Leadership, shugaban NBA ya ce:

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan

"An tabbatar mani da cewa yayin zaman kotu a jiya (Alhamis), ginin motsa, na kira magatakardar kotun kuma ta tabbatar min cewa Mai Shari’a Onyeukwu ya koka da lamarin kuma ya shaida mata abin da ya faru."

Ya kara da cewa, wani alkalin kotu ya shaida masa cewa hakan ya faru kwana biyu da suka gabata, kuma tun kafin a fara amfani da wannan ginin, an riga an yi korafi kan matsalolinsa amma ba a dauki mataki ba.

NBA: Lauyoyi sun dakatar da amfani da wurin

"Saboda haka, muna cewa a dakatar da amfani da wannan ginin na akalla mako guda, har sai an duba matsalar kuma kwararru sun tabbatar da cewa ginin yana da inganci.
"Ba za mu jefa rayukanmu cikin hadari ba. Mako daya ba zai kashe mu ba, bari a dakatar da ayyuka a wannan ginin," in ji Ihentuge.

Kotu ta soke naɗin sarki a Ogun

Kara karanta wannan

Jama'a sun farmaki masu lalata wutar Najeriya cikin dare, an kama wani ja'iri

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun jihar Ogun mai zama a Abeokuta ta soke naɗin sarkin Olawo, Alexander Macgregor, ta ce gwamna ya karya doka.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Majekodunmi ta bada umarnin kwace dukkan takardu, sandar mulki, da sauran alamomin sarauta da aka bai wa Macgregor.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel