'Yan Bindiga Sun Shiga Uku a Najeriya, Dakarun Sojoji Sun Hallaka Sama da 350

'Yan Bindiga Sun Shiga Uku a Najeriya, Dakarun Sojoji Sun Hallaka Sama da 350

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji ƴan ta'adda, sun aika wasu barzahu a watan Janairu, 2025 wanda zai ƙare a yau Juma'a
  • Mai magana da yawun hedkwatar sojoji ta ƙasa watau DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce dakaru sun hallaka ƴan ta'adda 358 a wata ɗaya
  • Buba ya ce dakarun sojin sun kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da dama sannan sun daƙile yunƙurin satar ɗanyen mai a Kudancin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 358 tare da kama mutane 431 da ake zargi a watan Janairu 2025.

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar tsaro watau DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a, 31 ga Janairu.

Kara karanta wannan

"An mari babban jigo," Jami'an tsaro sun mamaye hedkwatar PDP ta ƙasa a Abuja

Sojojin Najeriya.
Sojojin sun murkushe yan ta'adda sama da 300 a watan Janairun 2025 Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Getty Images

Ya ce wannan na ɗaya daga cikin nasarorin da dakarun sojojin suka samu a ƙoƙarin da suke yi na yaki da ƴan ta'adda a ƙasar nan, Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ceto mutane 249 da aka sace

Baya ga hakan, Buba ya ce sojojin sun kuma cafke mutane 59 da ake zargi da sata da fataucin danyen mai, tare da ceto mutane 249 da aka yi garkuwa da su.

A kudancin Najeriya, sojojin sun daƙile yunƙurin satar danyen mai da darajarsa ta haura Naira biliyan biyu (N2bn), a cewar rahoton Leadership.

Dakarun sun kwato makamai a Najeriya

Har ila yau, dakarun sun kwace makamai 370 da alburusai 4,972, wanda ya hada da bindigogi 105 na AK-47, bindigogi 25 da aka kera a gida da bindogin Dane guda 32.

Sauran makaman da dakarun sojojin suka kwato daga ƴan ta'adda a tsawon watan Janairu sun haɗa da bindiga mai carbi guda 23 da alburusai kala daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Sanarwar ta jaddada cewa sojoji za su ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da masu taimaka musu a fadin ƙasar, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sojoji sun hallaka yaran Bello Turji

A wani labarin, kun ji cewa sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta kan yaran kasurgumin ɗan ta'addan nan, Bello Turji a jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewaya ya ce sun sheke ƴan ta'adda masu ɗinbin yawa amma har yanzu ba su ga Turji ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262