Yan Bindiga Sun Fara Taɓa Manya, An Yi Garkuwa da Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Jiha
- Ƴan bindiga sun sace shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Abia watau ABSIEC, Farfesa George Chima
- Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun shiga har gida, suka sace shi yayin da ya karɓi bakuncin malaman jami'ar jihar Abia
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abia, Maureen Chinaka ta nemi a ba ta lokaci kafin ta ce wani abu kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Abia (ABSIEC), Farfesa George Chima.
Ƴan bindigar sun kutsa cikin gidan babban jami'in zaɓen da ke Okigwe a jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya, sannan suka yi awon gaba da shi.

Asali: Original
Yadda aka yi garkuwa da shugaban ABSIEC
Majiyoyi sun shaida wa jaridar Vanguard cewa ‘yan bindigar, kimanin su huɗu, sun farmaki gidansa a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu malamai daga jami’ar Abia, Uturu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun fara kokarin tafiya da shi a cikin motarsa, wacce direbansa ke wanke wa a lokacin amma ba su ci nasara ba.
Bayanai daga majiyoyi daban-daban sun nuna cewa duk da ƙoƙarin da suka yi na kunna motar amma ta ƙi tashi, hakan ya sa suka ƙwace wata mota.
Ganau ya shaida cewa, bayan motar ta ƙi tashi, ‘yan bindigar sun kwace wata mota da ke wucewa dauke da katako, suka tsere da shugaban ABSIEC.
Har yanzu ba a san inda suka tafi da shi ba, kuma babu wani bayani dangane da bukatun ‘yan bindigar na neman kudim fansa ko wani abu daban.
Yan sanda ba su ce komai ba tukuna
Da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a ta rundunar ‘yan sandan jihar Abia, Maureen Chinaka, dangane da lamarin, ta ce za ta yi karin bayani daga bisani.

Kara karanta wannan
'Ban son belin': Sowore ya buga da 'yan sanda, ya ce ya fi Tinubu karfin iko a baya
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan batun sace shugaban hukumar ABSIEC ba.
Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, musamman ma’aikatan hukumar zaɓe da kuma baƙin da ya yi a ranar daga Jami’ar Abia, inda ake fatan hukumomi za su hanzarta daukar matakan ceto shi.
Yan bindiga sun sace mutum 4 a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun sace mutum huɗu da suka kai farmami wata anguwa a yankin Kubwa da ke birnin tarayya Abuja.
An tattaro cewa dakarun ƴan sanda sun isa anguwar bayan sa'a ɗaya da harin ƴan bindigar saboda babu caji ofis a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng