Janar Abdulsalami Abubakar Ya Yi Magana kan Yiwuwar Dawowar Mulkin Soja a Najeriya
- Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya yi magana kan masu neman mulkin soja a Najeriya maimakon dimokuraɗiyya
- Janar Abdulsalami Abubakar ya yi magana ne bayan Najeriya ta kwashe shekaru 25 tana mulkin farar hula duk da ƙalubalen da kasar ke fuskanta
- A daya bangaren, shugaban majalisar dokokin Najeriya ya ce ƙarfafa jam’iyyun siyasa da adawa mai ma'ana na samar da shugabanci nagari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa sojoji ba za su sake komawa mulki ba domin zamanin mulkin soja ya wuce.
An ruwaito cewa Janar Abdulsalami ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da wani littafi a birnin tarayya Abuja.

Asali: Facebook
Jaridar the Nation ta wallafa cewa taron kaddamar da littafin ya tattaro manyan 'yan siyasa da masu fada a ji a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Janar Abdulsalami, dimokuraɗiyya ta zauna daram a Najeriya bayan shafe shekaru 25 tana ƙalubalantar matsin lamba daga ƙungiyoyin da ke adawa da mulkin farar hula.
Abdulsalami: Dimokuraɗiyya ta zauna daram
Janar Abdulsalami ya ce ba a taɓa samun wani lokaci a tarihin Najeriya da aka samu dimokuraɗiyya mai ɗorewa fiye da yanzu ba tun bayan samun ‘yancin kai a 1960.
Daily Trust ta wallafa cewa tsohon shugaban kasar ya ce:
“A bana, Najeriya za ta cika shekaru 26 tana tafiyar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba, kuma hakan ya nuna ƙarfin gwiwar 'yan Najeriya a kan tsarin farar hula.”
Tsohon shugaban ƙasar ya ce yana alfahari da kafa wannan tushe, inda ya miƙa mulki ga farar hula a ranar 29 ga Mayu, 1999, lokacin da ya bar mulki ga zababben shugaban ƙasa.
Bukatar cigaba da dimokuraɗiyya a Najeriya
Janar Abdulsalami ya bukaci ‘yan Najeriya da jam’iyyun siyasa da su cigaba da ba da gudunmawa wajen bunƙasa tsarin dimokuraɗiyya.
“Dole ne mu cigaba da nausa dimokuraɗiyya gaba a Najeriya domin ba mu da wani abu a madadin mulkin farar hula.”
- Janar Abdulsalami Abubakar
Ya kuma jaddada cewa nasarar da Najeriya ta samu a tsarin dimokuraɗiyya ya dogara ne da ƙarfin gwiwar jama’a da himmar shugabanni wajen gina tsayayyen tsari.
Bukatar karfafa jam’iyyun siyasa
A yayin taron, shugaban majalisar dokoki, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa dole ne a ƙarfafa jam’iyyun siyasa domin samar da shugabanci nagari.
A cewarsa, adawa mai ƙarfi da jam’iyyun siyasa masu nagarta na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci.
Ya kuma bukaci a daina amfani da ƙabilanci a siyasa domin cimma muradun kashin kai maimakon nuna kishi kasa.
Hukumar INEC ta yi kira ga ‘yan siyasa

Kara karanta wannan
'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci jam’iyyun siyasa da su tabbatar da dimokuraɗiyya a cikin tsarin su.
Shi ma shugaban dokoki, Tajudeen Abbas ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke ɗaukar jam’iyyun siyasa a matsayin hanya ta cimma burinsu na kashin kai.
El-Rufa'i ya gana da 'yan SDP a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya gana da shugannin jam'iyyar adawa ta SDP.
Shugaban jam'iyyar SDP na kasa ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan yadda za su kawo mafita ga Najeriya lura da halin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng