"Namiji ba Dan Goyo ba ne": Da Gaske Seaman Abbas Ya Saki Matarsa Hussaina?
- Seaman Abbas Haruna ya karyata rade-radin cewa ya saki matarsa Hussaina, yana mai cewa suna tare cikin soyayya da zaman lafiya
- Ya tabbatar da cewa matarsa ta kwanta asibiti har tsawon kwanaki 10 amma yanzu ta warke kuma tana shirin komawa gida
- Abbas ya ce babu wata matsala tsakaninsa da Hussaina kan kudin tallafi, yana zargin wasu ne ke kokarin haddasa rudani a tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Seaman Abbas Haruna, sojan ruwan Najeriya da aka sallama daga aiki ya yi magana kan rade-radin da ake yadawa cewa ya saki matarsa Hussaina.
A cikin wani bidiyonsa da ke yawo a kafofin sada zumunta, Seaman Abbas ya warware rudanin da aka samu game da zamantewarsa da Hussaina.

Asali: Facebook
Seaman Abbas ya saki matarsa Hussaina?
A bidiyon da Legit Hausa ta gani a shafin Dokin Karfe na Facebook, Seaman Abbas ya ce batun cewa ya saki matarsa Hussaina ba gaskiya ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sojan ya ce wasu ne kawai ke yada karairayi a kan cewa ya saki matarsa, yana mai cewa yanzu haka suna zaune cikin soyayya da juna.
Seaman Abbas ya ce:
"Na samun magana a kan ko na saki matata Hussaina, wannan maganar ba haka ba ne gaskiya, babu shi.
"Tsakani da Allah muna tare, muna zaman lafiya, ba wani abu da ya faru. Karairayi ne na mutane da suka shirya."
Seaman Abbas ya ce wadanda ke yada wadannan karairayin suna yi ne domin kawo wani rudani a tsakaninsu.
Hussaina ta yi rashin lafiya
Tsohon sojan ruwan ya kuma tabbatar da labarin da ake yadawa na cewar matarsa Hussaina ba ta lafiya kuma har ta shafe sama da kwanaki 10 a asibiti.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan
"Tabbas, akwai lokacin da aka kwantar da ita a asibitin Gombe, ta kai irin kwana goma sha. Likitoci sun yi kokari domin sun ba ta kulawa.
"Wannan shi ne gaskiya, ta yi rashin lafiya kuma ta samu sauki. Lokacin da za ta tafi gida aka ce ta koma gida ta samu sauki sosai sannan ta dawo mu ci gaba da zama."
- A cewar tsohon sojan.
Abbas Haruna ya shaida cewa yanzu haka 'ya'yansu na nan an sanya su a makaranta a Gombe, yayin da suke jiran dawowar Hussaina daga gidansu.
Tallafin kudi ya hada Abbas da Hussaina fada?
Hakazalika, Seaman Abbas ya yi tsokaci kan masu yada jita-jitar cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da Hussaina kan wasu kudade da aka ba su na tallafi.
Abbas ya ce:
"Ni wannan maganar babu shi. Sannan magana wai na an yi duka ba gaskiya ba ne. Ranar da za ta tafi, mun rabu bayan wasa da dariya."
Seaman Abbas ya tabbatar da cewa babu wani sabani tsakaninsa da matarsa, wasu bata gari ne kawai ke son kawo rudani da kuma tunzara matar.
'Yar fim ta yi gaggawar alkalanci
Sai dai, a hannu daya, jarumar Kannywood, Firdausi Yahaya ta ce zargin da ake yi wa Seaman Abbas ya nuna cewa namiji ba dan goyo ba ne.
A sakon da ta wallafa a shafinta na X, Firdausi Yahaya ta ce:
"Labarin seaman da matarsa ya kara nuna mana cewa maza ba yan goyo bane."
DHQ ta karyata tsare Seaman Abbas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta musanta zargin cewa an tsare Seaman Abbas, na tsawon shekara shida ba bisa adalci ba.
Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa, babu wani lokaci da aka kama Seaman Abbas kamar yadda matarsa ta bayyana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng