Bayan Dakatar da Shi daga Masallaci a Kano, DSS Ta Gayyaci Sheikh Bin Uthman
- Masallacin Jami’ur Rahman ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar sallah da yin wa’azi zuwa bayan kammala bincike
- Ana zargin hudubar da Bin Uthman ya gabatar ta jawo fushin jama’a, har ta kai ga kusan afkawa sakataren kwamitin amintattun masallacin
- Hukumar SSS ta gargadi Bin Uthman da gujewa hudubobi masu tayar da hankali, yayin da majalisar malamai ta ba shi shawara a kan dambarwar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Masallacin Jami’ur Rahman, wanda a da aka fi sani da Masjid Sahaba, ya dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar salla da yin wa’azi.
Dakatarwar ta biyo bayan hudubarsa ta ranar 24 Janairu, 2025, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce da kokarin tayar da husuma a tsakanin mabiya.

Kara karanta wannan
Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Asali: Facebook
Daily Nigerian ta wallafa cewa tsohon wurin masallacin, wanda Malam Bin Uthman ya shugabanta tsawon shekaru 24, yana dab da sabon wurin da aka kebe wa sanannen ɗan kasuwar mai, AY Maikifi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya bada filin, Maikifi ya gana da Bin Uthman, inda suka amince a haɗe shugabancin tsohon masallacin a sabon wurin da aka mallaka masa.
Hudubar da ta jawo dakatar da Bin Uthman
Leadership ta wallafa cewa yayin hudubar da ta janyo cece-kuce, Malam Bin Uthman ya bayyana cewa an mayar da shi saniyar ware a harkokin tafiyar da masallacin.
Ya ce masu gudanarwar masallacin sun naɗa sabbin limamai guda uku ba tare da an sanya shi a matsayin jagora ba.
Hudubar ta 24 ga watan Janairu ta fusata wasu daga cikin mabiya masallacin, har ta kai ga kusan afkawa sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Abdulkadir Isawa.
An dakatar da Sheikh Bin Uthman
Hukumar masallacin, a cikin wata wasika da daraktan kula da harkokin gudanarwa ya sanya wa hannu, ta dakatar da Bin Uthman har sai baba ta gani.
Haka kuma an umarce shi da ya mika duk wasu kayan masallacin da ke hannunsa zuwa ga hukumar gudanarwa.
A cikin wasikar, an ce:
“Muna mai tunatar da kai kan abin da ya faru bayan hudubar Jumu’a ta ranar 24 Janairu, 2025. A cikin hudubar, ka furta wasu kalamai da ke zubar da kima ga masallacin da yadda ake tafiyar da al’amuransa, wanda hakan ya janyo rikici bayan kammala sallah.”
“Saboda haka, ina sanar da kai cewa an amince da dakatar da kai daga shugabancin sallah har zuwa lokacin da bincike zai kammala. An kafa kwamiti da zai duba faifan bidiyo da sauti na hudubar da kuma jin bayanan wadanda suka shaida abin da ya faru.”
Hukumar DSS ta gayyaci Bin Uthman

Kara karanta wannan
Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take
A ranar Litinin, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) da Majalisar Malamai sun gayyaci Bin Uthman da kuma Alhaji AY Maikifi.
Majiyoyi sun bayyana cewa SSS ta gargadi Bin Uthman da gujewa hudubobi masu tayar da hankali da ka iya haddasa hargitsi a masallacin.
Majalisar Malamai, a nata bangaren, ta shawarci Bin Uthman da ya koma tsohon masallacinsa, sai dai babu tabbacin zai dauki wannan shawara.
Izala ta yi martani ga Bin Uthman
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Izalata kasa, reshen jihar Kano ta musanta zargin zaluncin da Sheikh Bin Usman ya yi zargin ana masa a sabon masallacin Sahaba.
Wanda ya gina masallacin, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi, ya ce wannan rikici sharrin shaidan ne kawai, yana mai kira ga bangarorin da ke sabani da su sasanta kansu cikin lumana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng