Hisbah: An Kama Ƴan 'Daɗi Soyayya' da Suka Yi Aure a Wurin Shakatawa a Kano

Hisbah: An Kama Ƴan 'Daɗi Soyayya' da Suka Yi Aure a Wurin Shakatawa a Kano

  • Hukumar Hisbah ta kama wasu ƴan daɗi soyayya, saurayi da budurwa da suka yi aure ba tare da izinin iyaye ko waliyyai ba
  • Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar ya ce matasan sun yi aure ne a wurin shaƙatawa
  • Kwamandan ya ce Hisbah ba za ta lamunci irin haka ba domin ya saɓawa shari'ar addinin Musulunci da al'adar mutanen jihar Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin ɗaura wa kansu aure a wani dandalin taro ba tare da izinin iyayensu ba.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, ne ya bayyana hakan a Kano.

Yan Hisbah.
Yan Hisbah sun cafke saurayi da budurwa da suka yi aure ba tare da izinin iyaye ba a Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

Ya ce matasan sun daura aurensu da kansu a wani wurin shakatawa, bayan wani mutum da ba su da wata alaka da shi ya biya sadakin amaryar, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kano: Saurayi da budurwa sun daurawa kansu Aure a Kano, Hisbah ta cafke su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hisbah ta kama saurayi da budurwa a Kano

Wannan abu, a cewarsa, ya saba wa koyarwar addinin Musulunci da al’adun mutanen jihar Kano da ke Arewa maso Yamma.

Sheikh Mujahid ya bayyana cewa hukumar Hisbah ba za ta lamunci irin wannan abu ya ci gaba da faruwa ba.

Ya ce wannan aure ya saɓawa doka, kuma ya saba wa tsarin shari’a da Musulunci ya tanada.

Mataimakin kwamandan Hisbah ya kara da cewa auren dole ne ya samu izinin iyaye ko waliyyan amarya da wakilan ango, domin hakan shi ne abin da addini ya tanada.

"Ina so in sanar da jama’a cewa Hisbah ta kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don gano duk wanda ke da hannu a wannan lamarin," in ji shi.

Hisbah na ƙoƙarin kama masu hannu a lamarin

Ya kuma bayyana cewa hukumar na kokarin kama abokan ma’auratan da duk wanda ya taimaka wajen shirya wannan aure don hana afkuwar irin haka a nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Ya yaba da irin kokarin da jama’a suka yi na sanar da hukumar Hisbah game da wannan abu, yana mai kira da su ci gaba da bayar da hadin kai don dakile irin wadannan abubuwa da ba su dace da al’ada da addini ba.

'Yan Hisbah ta gargaɗi masu caca a Kano

Kun ji cewa hukumar Hihbah ta lashi takobin sa kafar wando ɗaya da duk wasu masu yin caca a Kano bayan hukuncin kotun ƙolin Najeriya.

Rundunar ƴan sandan Musulunci ta ce ba za ta lamurci yin caca ba a faɗin jihar, don haka ta gargaɗi masu yi su gaggauta tuba su daina.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel